Kano: Ɗan Sarauniya ya nemi gafarar Gwamnan Ganduje kan ɓata masa suna a Facebook
- Tsohon kwamishinan ayyuka da tsare-tsare na jihar Kano, Muaz Magaji, ya aike da sakon neman yafiya ga gwamna Ganduje
- Injiniya Magaji, wanda aka fi sani da Ɗan Sarauniya ya samu saɓani da gwamnan ne bayan yin wani rubutu a Facebook da ya taɓa kimar Ganduje
- Ya ba gwamna da iyalansa hakuri tare da bayyana cewa ba ya yi hakan da nufin ɓata sunan iyalan gwamnan da shugabancinsa ba
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kano - Tsohon kwamishinan ayyuka a jihar Kano, Injiniya Mu'azu Magaji, wanda aka fi sani da Ɗan Sarauniya ya bai wa gwamna Abdullahi Umar Ganduje hakuri kan abin da ya faru.
Tsohon kwamishinan ya gurfana a gaban Kotun Majistire a Kano kan wani rubutu da ya yi a Facebook da ake zargin cin mutunci ne ga gwamna da iyalansa.
Bayan haka kuma aka cigaba da tsare shi a gidan gyaran hali har zuwa lokacin da Kotu ta amince ta ba shi Beli.
Watanni biyar bayan rubutun wanda ya ta da hayaniya, tsohon kwamishinan ya sake komawa dandalin Facebook domin neman afuwar gwamna da iyalansa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Magaji ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa:
"Bayan laifin da na maka a shafin Facebook nake ganin ya dace na dawo kafar da na yi domin neman afuwarka. Ina mai rubuta sakon neman afuwa ga mai girma gwamna kan rubutun da na yi a Facebook a farkon watan Janairu, 2022."
"Rubutan wanda ka iya jawo bacin ran gwamna da iyalansa da kuma kallon abun ta hanyar da ba ita na nufa ba wacce zata iya taɓa mutuncin gwamna da jagorancinsa."
"Ina mai ƙanƙan da kai tare da ba da hakuri kan bacin rai da cutarwar da rubutu na ba da nufi ba ka iya jawowa da taɓa gwamna da kuma iyalansa."
Yaushe ne mafarin lamarin?
Tsohon kwamishinan ya shiga batutuwan tattaunawa ne a 2020 bayan gwamna Ganduje ya tsige shi daga kujerarsa kan abin da gwamnati ta ayyana da wuce gona da iri.
Hakanan an zargi Ɗan Sarauniya da murnar rasuwar Abba Kyari, shugaban shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Buhari.
A 2021, ya fice daga jam'iyyar APC, ya koma jam'iyyar People Democratic Party wato PDP, inda ya nemi takarar gwamna amma ya rasa tikiti.
A wani labarin kuma Alarammoni da wasu dubbannin mutane sun gudanar da Addu'a kan zaɓen 2023 a Kano
Dubbanin musulmai a Kano sun gudanar da Addu'o'in samun zaman lafiya da gudanar da zaɓen 2023 cikin kwanciyar hankali.
Mutanen da suka haɗa da Alarammoni sun kuma yi Addu'o'in Allah ya zaɓa wa Najeriya shugaban ƙasa nagari.
Asali: Legit.ng