Shugaba Buhari zai yiwa yan Najeriya jawabi na musamman gobe Lahadi
1 - tsawon mintuna
- Albarkacin ranar demokradiyya, Shugaba Buhari zai yiwa yan Najeriya jawabi gobe da sassafe
- Shugaba Muhammadu Buhari ne ya sauya ranar demokradiyya daga 29 ga Mayu zuwa 12 ga Mayu
- An bukaci yan Najeriya su dasa kunne gobe misalin karfe bakwai na safe don sauraron shugaban kasa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari zai yiwa yan Najeriya jawabi ta musamman misalin karfe 7 na safiyar Lahadi, 12 ga watan Yuni, 2022.
Ministan Labarai, Lai Mohammed, ya bayyana hakan yayin hira da yan gidan rediyo ranar Alhamis a Abuja.
Lai Mohammed yace zai yi jawabin bisa murnar ranar demokradiyya ta shekarar nan.
Hadimin shugaban kasa kan gidajen rediyo da talabijin, Buhari Sallau, ya bayyana cewa misalin karfe 7 na safe Shugaba Buhari zai yiwa yan Najeriya jawabin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng