Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari na jagorantar zaman shawo kan matsalar tsaro
- Yanzun nan muke samun labarin cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar taro da tawagar tsaron Najeriya
- Ana kyautata zaton tawagar za ta tattauna da Buhari ne kan habaka hanyoyin ragargazar makiya kasar
- Najeriya dai na fuskantar matsalolin tsaro da dama, kama daga yankin Arewa har zuwa Kudancin kasar
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar taron majalisar tsaron kasar nan a fadar shugaban kasa da ke Abuja, The Nation ta ruwaito.
Ana sa ran taron zai tattauna batutuwan da suka shafi dabarun bunkasa nasarorin da aka samu a baya-bayan nan wajen yaki da ta'addanci da rashin tsaro gaba daya.
Taron ya samu halartar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; Sakataren Gwamnatin Tarayya; Boss Mustapha da Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.
A gefe guda akwai mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya).
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor, Babban Hafsan Sojoji, Laftanar Janar Farouk Yahaya; Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo; da babban hafsan hafsoshin sojin sama Air Marshal Isiaka Oladayo Amao suma sun halarci taron.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Alkali Baba Usman; Babban Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS), Yusuf Bichi; da Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ahmed Rufa'i Abubakar.
Karin bayani na nan tafe...
Asali: Legit.ng