An gurfanar da wani matashi kan satar Fankar Masallaci a Bauchi, an yanke masa hukunci
1 - tsawon mintuna
- An cika hannu da wani matashi a jihar Bauchi kan laifin satar fanka a Masallaci
- Kotun Shari'a dake jihar ta yanke masa hukuncin daurin wata goma sha biyar a gidan kurkuku
- Jihar Bauchi na daya daga cikin jihohin Arewacin Najeriya da akwai kotunan Shari'ar Musulunci
Bauchi - An damke wani mutumi mai suna Salisu Aliyu kan zargin satar Fanka a cikin Masallacin garejin motar Dass dake karamar hukumar Dass, jihar Bauchi.
Ba tare da bata lokaci ba an gurfanar da matashin dan shekara 25 gaban kotun Shari'a ta biyu dake jihar, rahoton Leadership.
A kotu, Salisu Aliyu, ya amsa laifin cewa lallai ya aikata wannan laifi.
Alkalin kotun, Mukhta, ya jefashi kurkukun daurin watanni 15 a gidan kaso amma an bashi zabin biyan tara N30,000 da bulala 50.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng