An yi kutse a shafin NNPC na Twitter, an yi amfani da shi wajen hasashen abokin takarar Tinubu
- Shafin kamfanin NNPC na Twitter ya yi martani ga wata wallafa da aka yi a shafin cewa dan takarar shugaban kasa na APC, Tinubu, zai zabi mataimakin shugaban kasa Musulmi
- Sai dai kuma tuni aka goge rubutun wanda hakan na nuna cewa mai kula da shafin ya manta bai sauya shi zuwa nashi na kashin kansa ba kafin ya yi martanin
- NNPC ya kuma fitar da wani jawabi inda yake nesanta kansa da rubutun yana mai cewa an yi kutse ne amma sun shawo kan abun
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Shafin kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) a ranar Laraba, 8 ga watan Yuni, ya wallafa wani sako game da abokin takarar Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Tinubu ya samu kuri’u 1,271 wajen kayar da sauran abokan karawarsa a zaben fidda gwanin APC wanda aka kammala a ranar Laraba.
Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri kuma babban abokin karawarsa, ya samu kuri’u 316 yayin da mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya samu kuri’u 235.
Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, ya samu kuri’u 152, yayin da Yahaya Bello, Gwamnan jihar Kogi ya samu kuri’u 47.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A ranar Laraba, wani mai amfani da shafin Twitter @Ssaasquatch, ya wallafa yadda Tinubu zai iya kasancewa a tsaki mai wuya wajen zabar dan takarar mataimakin shugaban kasa.
Da yake martani ga wallafar, shafin hukumar NNPC ya rubuta:
“Zai yi takara ne da mataimakin shugaban kasa Musulmi.”
Wallafar wanda da dukkan alamu an yi sa ne bisa kuskure, ya rigada ya samu fiye da mutane 90 da suka sake yada shi.
Ta yiwu mai kula da shafin ya manta bai sauya shafin zuwa nasa na kashin kansa bane.
Sai dai kuma, tuni aka goge rubutun.
An yi kutse a shafinmu na Twitter - NNPC
Sannan kamfanin na NNPC ya fitar da sabon sako da ke nesanta kansa daga rubutun.
Sanarwar ya ce:
“Ana sanar da jama’a cewa an yi kuntse a shafin @NNPCgroup na Twitter sannan aka yi amfani da shi wajen tura sakon da bai dace ba a ranar 8 ga watan Yuni 2022 da misalin karfe 6:35 na yamma. An magance lamarin kutsen, kuma an yi nasarar dawo da shafin.
“#NNPCLimited na fatan sake tabbatar da jama’a cewa tana ci gaba da jajircewa wajen yin kasuwanci yadda ya kamata a dukkan lokuta.”
Tinubu ya karyata labarin ‘sharrin’ da ake yi masa ana tsakiyar zaben ‘Dan takara a APC
A baya mun ji cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya karyata labarin da yake yawo a halin yanzu a game da zabinsa na ‘dan takarar mataimakin shugaban Najeriya.
A wata sanarwa da ta fito wanda ta shigo hannun Legit.ng Hausa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ce babu gaskiyar cewa zai dauko Musulmi ne a tikitinsa.
Sanarwar ta fito ne daga ofishin yakin neman zaben Bola Tinubu a ranar Talata, 7 ga watan Yuni 2022.
Asali: Legit.ng