Ana gab da zaben fidda gwani, Babban Hadimin Buhari ya gana da Jonathan a Abuja

Ana gab da zaben fidda gwani, Babban Hadimin Buhari ya gana da Jonathan a Abuja

  • Kakakin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya gana da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan
  • Shehu ya bayyana cewa dukkan su sun ji daɗi kuma sun nuna wa juna ƙauna a Otal ɗin Fraser Suites Hotel, Abuja
  • A farkon gwamnatin shugaban Buhari, Malam Shehu na ɗaya daga cikin masu sukar Jonathan kan abubuwa da dama

Abuja - Babban mai magana da yawun shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya gana da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ranar Alhamis a Abuja.

Malam Shehu ne ya bayyana haka a wani rubutu da ya yi a shafinsa na dandalin sada zumunta Twitter, tare da tura Hotonsa tare da tsohon shugaban ƙasan.

Garba Shehu da Jonathan.
Ana gaba da zaben fidda gwani, Babban Hadimin Buhari ya gana da Jonathan a Abuja Hoto: @garshehu
Asali: Twitter

Shehu ya ce:

"Yanzu na garzaya wurin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a wurin wani taro da yammacin nan a Fraser Suites Hotel, Abuja. Ya tarbe ni cikin soyayya da ƙauna."

Kara karanta wannan

Tinubu ya saki sabon Bidiyo, ya faɗi inda zai nufa idan ya sha ƙasa a zaɓen fidda gwanin APC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin shugaban ƙasa Buhari na ɗaya daga cikin mutanen da suka ɗauka da zafi kan Jonathan a farkon wa'adin wannan gwamnatin.

A wancan lokacin, Shehu ya zargi tsohon shugaban ƙasan da laifin tsaikon da aka samu na jinkirin Buhari gabanin naɗa mambobin majalisar zartarwa a gwamnatinsa.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa sai da shugaba Buhari ya shafe watanni Shida kafin ya bayyana mambobin gwamnatinsa, wanda hakan ya ja masa suka a ƙasa.

Amma Shehu ya ce Kwamitin karɓan mulki bai samu cikakken haɗin kai daga gwamnatin Jonathan ba kuma hakan ne ya shafi sabuwar gwamnatin Buhari.

Sukar tsohon shugaban ta ragu yayin da Goodluck Jonathan ya fara ɗasa wa da shugaban ƙasa Buhari.

Ina zancen takarar Jonathan a APC?

An jima ana alaƙanta Jonathan da shiga tseren takarar shugaban ƙasa karkashin APC, inda wasu gwamnononin cigaba na jam'iyya mai mulki ke goyon bayan ya gaji Buhari.

Kara karanta wannan

2023: Na fi kowa tsammanin lashe tikitin takarar shugaban ƙasa a APC, Gwamnan Arewa

Rashin halartar babban taron jam'iyyar PDP na ƙasa ya ƙara wa jita-jitar da ake yaɗawa taki cewa ya juyawa babbar jam'iyyar hamayya baya.

Amma Jonathan bai halarci wurin da jam'iyyar APC ta gudanar da aikin tantance yan takararta na shugaban ƙasa ba.

A wani labarin na daban kuma Rikici ya ɓarke a Sakatariyar APC ta Abuja bayan ɗan takarar shugaban kasa ya jefa kyautar N50,000

Danbarwa ta barke tsakanin direbobi, jami'an tsaro da masoyan APC bayan gwamna Umahi ya watsa kyautar N50,000 a Abuja.

Bayanai sun bayyana cewa ɗan takarar shugaban ƙasan ya watsa kudin ne yayin da yake gab da shiga Mota a Sakatariyar APC ta ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel