Gumi ya bukaci FG ta kafa ma'aikatar harkokin makiyaya don jin kokensu

Gumi ya bukaci FG ta kafa ma'aikatar harkokin makiyaya don jin kokensu

  • Fitaccen malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Dr Ahmad Gumi ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da ma'aikatar da za ta dinga kula da lamurran makiyaya don kawo karshen matsalolinsu
  • Ya fadi hakan ne yayin jawabi ranar Laraba a taron makiyaya da bada tsaro ga Fulani wanda ya gabata na kungiyar Miyetti Allah ta Najeriya da kungiyar sasanci ta arewa suka gabatar a Abuja
  • Haka zalika, shugaban kungiyar MACBAN, Husseini Bosso ya koka a kan irin kalubale da suke fuskanta a harkar noma da kiwonsu amma duk da haka gani ake kamar su ne ke da alhaki a ta'addanci bayan su yafi shafa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Ahmad Gumi, fitaccen malamin addinin musuluncin nan, ya yi kira ga gwamnatin tarayya samar da ma'aikatar da za ta dunga lura da lamurran makiyaya don kawo karshen matsalolinsu.

Kara karanta wannan

Deliget din PDP ya sadaukar da dukkan kudin da ya samu ga al'ummarsa, ya biya wa yara kudin makaranta

Gumi ya fadi hakan ne a ranar Laraba a 'taron makiyaya da bada tsaro ga Fulani ', wanda ya gabata a Abuja mai taken, 'Mafita ga kalubalen tsaro ga makiyaya da Fulani a Najeriya.'

Kungiyar Miyetti Allah ta makiyayan shanu da Kungiyar Sulhu ta arewa (NCM) ne suka shirya taron, The Cable ta ruwaito.

Gumi ya bukaci FG ta kafa ma'aikatar harkokin makiyaya don jin kokensu
Gumi ya bukaci FG ta kafa ma'aikatar harkokin makiyaya don jin kokensu. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A cewar malamin, makiyayan fulani da sauran kungiyoyin sun cancanci kula irin wacce ake bawa yan Neja Delta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ya kamata gwamnati ta maida hankalinta a kan wadannan mutanen saboda yadda suke yawan bayyana damuwarsu," NAN ta yanko maganarsa inda yake cewa.
"Abun da na tsammata daga gwamnati bai gaza da abun da tayi ba, a lokacin da matasan Neja Delta na barnatar da tattalin arzirki.
"Wadannan mutanen suma suna addabar arzikin noman Najeriya wanda shi ne tushen tattalin arzirkin kasar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe makiyaya 4, sun sace shanaye 60 a Anambra

"A ganina akwai bukatar gwamnati ta kara kulawa. Suna bukatar a mai da hankali a kansu. Mafi karancin abun da suke bukata shine ma'akatar da zata lura da lamarinsu."

Husseini Bosso, shugaban MACBAN na kasa, yayin jawabinsa, ya ce ya wuce a ce labari ne garkuwa da mutane da fashi da makami wanda ya zama ruwan dare a yankuna da dama a kasar nan.

Sai dai, Bosso ya ce ba gaskiya bane jita-jitar da ake yadawa na cewa makiyaya ne ke da alhakin wadannan ta'addancin, suma makiyayan na fuskantar kalubalen.

"Abun takaici shi ne yadda ba a yada duk wani farmaki da ya ritsa da makiyaya a yanar gizo. Mutanenmu sun fi kowa fuskantar matsalar tsaro," a cewarsa.
"Cikin kwanakin nan aka yi garkuwa gami da halaka shugabannin MACBAN na Kogi, Neja, Nasarawa da shugabannin kananan hukumomi biyar, wadanda suka hada da gundumar Gwagwalada.
"Hakan na nuna cewa ba mu tsira daga matsalolin garkuwa da mutane da fashi da makami a yankunanmu ba."

Kara karanta wannan

Bayan kwana 40, 'dan Najeriya da ya tuko babu daga London ya iso Legas, hotunansa sun bayyana

Sheikh Gumi ya kafa kungiyar kare hakkin Fulani Makiyaya

A wani labari na daban, fitaccen malamin addinin Musulunci, Ahmad Gumi, ya sanar da cewa ya kafa kungiyar assasa kare hakkin Fulani makiyaya.

Gumi ya bada sanarwan kafa kungiyar wacce za a kira ta da Nomadic Rights Concern (NORIC) a yayin tafsirin watan Ramadan a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna.

Ya ce kungiyar za ta tattaro tare da bayyana irin cin zarafi da take hakkokin Fulani makiyaya da ake yi, Premium Times ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng