Ramin Mugunta: Bam Da IPOB Ta Birne a Hanya Ya Tashi Da Mambobinta a Imo

Ramin Mugunta: Bam Da IPOB Ta Birne a Hanya Ya Tashi Da Mambobinta a Imo

  • Wasu mutane biyu da ake zargin mambobin haramtaciyar kungiyar IPOB/ESN ne sun yi munanan rauni yayin da wani bam ya tashi a ranar Laraba 1 ga watan Yuni
  • Mutanen biyu, a cewar Rundunar Sojojin Najeriya, sun taka bam din da suka birne ne bisa kuskure a hanyoyi a garin Orlu
  • Rundunar sojojin ta Najeriya ta bukaci mutanen yankin na kudu maso gabas masu son zaman lafiya su rika sanar da sojojin wuraren da suke zargin an binne bama-bamai

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Imo - Wani abin fashewa/bam da aka rahoto cewa mambobin kungiyar IPOB/ESN ne suka birne ya fashe, ya kuma yi wa mambobin kungiyar biyu mummunan rauni, rahoton NAN.

A cewar Vanguard, lamarin ya faru ne a kan hanyar Eke Ututu - Orsu a karamar hukumar Orsu a Jihar Imo a ranar Laraba 1 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Kai Samame Maɓuyar Masu Garkuwa, Sun Ragargajesu Sun Ceto Mutane

Ramin Mugunta: Bam Da IPOB Ta Birne a Hanya Ya Tashi Da Mambobinta a Imo
Bam Da IPOB Ta Birne a Hanya Ya Tashi Da Mambobinta Biyu a Imo. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojoji, Brig Janar Onyema Nwachukwu ya fitar ta ce:

"Bata garin, sun taka wani abin fashewa da suka birne a baya a kan hanyar karamar hukumar Orlu, yayin da suke kokarin tserewa daga dakarun sojoji da ke farautarsu a yankin.
"Haramtaciyyar kungiyar ta birne bama-bamai da dama a hanyoyin da sojoji ke sintiri amma ba su yi nasarar raunata sojojin ba.
"Muna kira ga mutanen Kudu maso Gabas masu son zaman lafiya su rika sanar da sojoji wuraren da suke zargin an birne bama-baman domin a cire su tare da zubarwa."

'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed

A bangare gudan, Gwamnatin Tarayya, a ranar Laraba ta ce yan ta'addan da suka kai hari sansanin sojoji da ke Birnin Gwari a Kaduna sun sha azaba a hannun sojoji a yayin da suka fatattake su, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Rikici: Tsagerun IPOB sun mamaye makarantu, sun fatattaki dalibai saboda wani dalili

Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyi kan tsaro bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Aso Villa a Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa sojoji 11 ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka jikkata yayin harin na ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel