Almundahanan Akanta Janar N80bn: Duk laifin Buhari ne, Buba Galadima

Almundahanan Akanta Janar N80bn: Duk laifin Buhari ne, Buba Galadima

Tsohon mamban kwamitin amintattun jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Buba Galadima, ya yi Alla-wadai da yadda ake sama da fadi da kudin kasa karkashin Shugaba Muhammadu Buhari.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Galadima ya ce kama Akanta Janar, Ahmed Idris, wanda ake zargi da satan N80bn ba shi ke nuna gwamnatinsa na yaki da rashawa ba.

Dattijon ya bayyana hakan ne a hirarsa da tashar ChannelsTV.

Yace:

"Shin wai kun yarda mutumin nan na yaki da rashawa ya sa aka kama Akanta-Janar? Sau nawa ana kai masa karar Akanta Janar?"
"Saboda abin ya wuce gona da iri ne yasa aka kamashi. Wannan ba shi bane karon farko. Wa'adin Akanta-Janar ya kare amma ya barshi ya cigaba da zama a ofis."
"Shin wa'adinsa bai kare bane? Shekaru biyu da suka gabata? Me yasa ya barshi a ofis? Shin yana jika wasu makusantan Buhari da kudi ne?

Kara karanta wannan

Rudani: Sabbin bayanai sun fito, yayin da gwamnonin APC ke shawari kan zaban magajin Buhari

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Galadima yace duk wanda ya gaji Buhari na da aiki a gabansa.

Buba Galadima
Almundahanan Akanta Janar N80bn: Duk laifin Buhari ne, Buba Galadima Hoto: Engr Buba Galadima
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel