Ba gaskiya bane: Rundunar soji ta magantu kan labarin barnar da 'yan ta'addan Kamaru suka yi a Najeriya
- Rundunar sojin Najeriya ta yi watsi da batun cewa wasu yan ta’addan kasar Kamaru sun farmaki garuruwan Najeriya
- A wata sanarwa da ta saki a ranar Litinin, 30 ga watan Mayu, rundunar sojin ta ce garuruwan da mayakan suka farmaka ba a Najeriya suke ba
- Ta kuma ce dakarunta da jami’an hukumar kula da shige da fice sun ceto wasu da lamarin ya ritsa da su bayan sun tsallako Najeriya
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Rundunar sojin Najeriya ta yi watsi da rahotannin cewa yan ta’addan kasar Kamaru sun farmaki wasu kauyukan Najeriya a ranar Lahadi, 29 ga watan Mayu.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya yi watsi da ikirarin a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Litinin, a Abuja, Nigerian Tribune ta rahoto.
Nwachukwu ya ce dakarun sojin Najeriya da aka tura Danare sun samu labari a safiyar ranar Lahadi game da harin da ake magana a kai.
Ya ce nan take aka tura dakarun zuwa garin Bashu, wanda aka yi zargin cewa yana karkashin hari.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce:
“Da isarsu, sai aka bayyana cewa Bashu baya karkashin hari, maimakon haka mayakan sun farmaki Obonyi 2 da Njasha, wanda dukkansu garuruwan Kamaru ne.
“Daga bisani, dakarunmu da jami’in hukumar shige da fice ta Najeriya sun yi nasarar ceto mutane hudu da abun ya ritsa da su, wadanda suka tsallako kasar Najeriya.
“Don haka harin bai wakana a cikin Najeriya ba kamar yadda aka yi ikirari.”
Nwachukwu ya bukaci jama’a da kada su tayar da hankalinsu ta hanyar yin watsi da wannan labarin.
Ƴan ta'addan ƙasar Kamaru sun shigo Najeriya, sun bindige rayuka 20
A baya mun ji cewa tsagerun Ambazonia, wata kungiyar 'yan aware ta kudu maso yammacin kasar Kamaru, ta halaka rayuka a kalla 20 a cikin al'ummar karamar hukumar Boki ta jihar Cross River a Najeriya.
Chief Cletus Obun, tsohon dan majalisar jihar Cross River kuma dan takarar kujerar majalisar wakilai ta Boki da Ikom ne ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce lamarin ya faru ranar Lahadi.
Ya ce ragowar 'yan kasar Kamarun wadanda su ke yin yaren Bokye na jama'ar Boki sun cika yankin Bashu, wani gari da ba shi da nisa da Danare, inda dakarun sojin Najeriya ke da karamin sansani, Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng