Sanata ya kwace motocin da ya rabawa Deleget bayan fadi zaben fidda gwani

Sanata ya kwace motocin da ya rabawa Deleget bayan fadi zaben fidda gwani

  • Shugaban kwamitin korafe-korafe a majalisar dattawa ya sha kaye a zaben fidda gwanin yunkurin komawa majalisa
  • Daga fadi, ya fara bin wadanda ya rabawa motocin kamfe yana kwace kyaututtukan da ya basu
  • Ya bayyana cewa bai taba tunanin deleget zasuyi masa hakan ba duk da kokarin da yake yiwa mazabar

Ondo - Yan kwanaki bayan fadi zaben fidda gwanin dan takaran Sanata mai wakiltar Ondo ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Ayo Akinyelure, ya kwace motocin da ya baiwa wasu jigogin jam'iyyar People’s Democratic Party PDP a jihar.

Akinyelure wanda ke wakiltan ta tsakiya ya sha kaye hannun Ife Adedipe SAN.

Ya samu kuri'u 58 yayinda wanda ya lallasa shi ya samu kuri'u 82.

Yana fadi ya bibiyi jigogin siyasa ya kwace motocin da ya raba musu, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike: Da Na So, Da Na Tarwatsa Jam'iyyar PDP a Daren Asabar, Hakuri Kawai Nayi

A cewar wani jigon PDP, yace Sanatan ya kwace motar da ya baiwa Cif Segun Adegoke, wani mamban kwamitin amintattatun PDP da kuma Hon Wole Akindiose, wani tsohon shugaban jam'iyyar PDP kuma Deleget na kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata
Sanata ya kwace motocin da ya rabawa Deleget bayan fadi zaben fidda gwani Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

Amma mai magana da yawun Sanatan, Charles Akinwon, yace motar mutum daya kawai suka kwace.

Yace motar Akindiose aka kwace saboda bai cika alkawarin da yayi ba na zaben fidda gwanin.

Yace:

"Barista Akindiose ya yi alkawarin lamunce wa Sanata Ayo Akinyelure dukka deleget din Ondo East/West kuma ya gaza yin hakan, bal ko kuri'arsu daya bai samu ba."

Sun yaudare ni, Sanatan Ayo

Akinyelure ya bayyana cewa duk da abubuwan da yayiwa al'ummar yankin, haka deleget zasu yi masa saboda wasu manyan yan siyasa sun fada musu suyi hakan.

Yace:

"A matsayin na na babban Sanata da kuma dukkan abubuwan da na musu a mazabar Ondo ta tsakiya."

Kara karanta wannan

Sanatan APC: Gwamna Wike ya yi kokari, shi ya ci zaben fidda gwani ba Àtiku ba a ra'ayina

"Ban taba tunanin da haka zasu biyani ba. Amma kaddara ce."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng