Yadda aka tsinci gawarwakin wani dan kasuwa, matarsa da yaransu 3 baje a gidansu
- Al'ummar yankin Apapa da ke jihar Lagas sun shiga wani yanayi bayan an tsinci wani dan kasuwa, Lawrence Olorungbon, matarsa da yaransa uku a mace
- An gano gawarwakin nasu wanda ya riga ya rube a cikin gidansu bayan da sakatariyar mutumin ta ziyarce su
- Sakatariyar ta shiga damuwa lokacin da ta dungi kiran layin ubangidan nata amma baya shiga, don haka sai ta yanke shawarar duba shi a gidansa
Lagos - Rahotanni sun kawo cewa an tsinci gawarwakin wani dan kasuwa, Lawrence Olorungbon, matarsa da yaransu uku a cikin gidansu da ke yankin Apapa ta jihar Lagas.
Zuwa yanzu ba a san musababbin mutuwarsu ba yayin da jami’an tsaron sashin manyan laifuka suka fara bincike don gano abun da ya haddasa faruwar wannan mummunan lamari.
Yadda aka gano faruwar lamarin
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa sakatariyar marigayin mai suna Njoku Treasure, ta yi kokarin kiran ubangidan nata a wayar tarho a ranar Laraba da ya gabata amma bata same shi ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Hakan ya sanya washegari ta sake kokarin kiransa amma bai je ba, wannan ne yasa ta kai ziyara gidansa da ke Apapa, amma kawai sai ta tarar da kofar gidan kulle da makulli.
A rahoton The Eagle, sakatariyar ta ce ta ji wani wari mara dadi yana fitowa daga gidan yayin da kudaje suka cika a kewayen gidan.
Nan take sai ta sanar da yan sandan Apapa wadanda suka ziyarci wajen sannan suka balla kofar gidan, kawai sai suka tarar da gawarwakinsu wadanda sun rigada sun rube.
Ni ne nan namijin duniya: Wani bakin fata ya saki hotunan yara 33 da ya haifa da yan mata daban-daban
A wani labari na daban, wani bakin fata da aka ambata da suna Demond George ya haddasa cece-kuce a shafin soshiyal midiya bayan ya nuna yara 33 da ya haifa.
A wata wallafa da ya yi a shafin Facebook a ranar Litinin, 23 ga watan Mayu, Desmond ya nuna hotunan yaransa sanye da tufafi mai launin baki iri daya dauke da rubutun ‘The LEGACY’ rubuce a gaba.
A wallafar tasa, Demond ya ce ‘wannan gadon zai ci gaba har abada’ yayin da ya bayyana sunayen wasu mutane da suka saka wannan daukar hoto nasu ya tabbata.
Asali: Legit.ng