Yan bindiga sun ƙona motoci uku a wani kazamin hari da suka kai jihar Katsina

Yan bindiga sun ƙona motoci uku a wani kazamin hari da suka kai jihar Katsina

  • Wasu tsagerun yan bindiga da yawan gaske sun farmaki shingen bincike na jami'an tsaro a yankin Jibiya jihar Katsina
  • Wasu bayanai sun nuna cewa maharan haye kan Babura sama da 200 sun yi ajalin direba kuma sun kona motoci uku
  • Kakakin hukumar Kwastan na Katsina, Isa Ɗanbaba, ya tabbatar da kai harin da kuma ɓarnar da maharan suka tafka

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Katsina - Wasu yan bindigan daji sun farmaki shingen binciken jami'an tsaro da ke Mil Takwas, yankin Jibiya, wanda ba shi da nisa sosai zuwa cikin birnin Katsina.

Wata majiya ta shaida wa Daily Trust cewa Gomman yan bindigan sun fito ne daga yankin Bugaje, amma wani ɗan Acaɓa ya ankarar da jami'an tsaron da ke Shingen game da motsin maharan.

Yan bindiga sun kai hari Katsina.
Yan bindiga sun ƙona motoci uku a wani kazamin hari da suka kai jihar Katsina Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya ce wasu dakarun sojoji suna wurin mintuna 30 kafin harin, sun bar wurin ne bayan samun rahoton gaggawa cewa wasu mahara sun nufi wani gati daga ƙauyen Tsambe.

Kara karanta wannan

Jirgin Abuja-Kaduna: Yan bindigan da suka sace Fasinjojin jirgi sun saki sabon Bidiyo, sun ba FG zaɓi biyu

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An samu bayanan sirri na motsin yan bindigan daga Bugaje saboda wasu sojoji na wurin domin gwabzawa, amma sai sojoji suka samu wani rahoton wasu gomman yan bindiga sun nufi Jibiya daga Tsambe, hakan yasa suka tafi tarar su."
"Bayan Mintuna 30 wani ɗan Acaɓa ya gaya wa Dakarun tsaron da ke wurin cewa yan bindiga sun nufo wajen Shingen, kuma bisa rashin sa'a kaɗan ke da bindiga dan haka suka tsere, maharan suka zo suka kone motoci uku."

Mutum nawa harin ya shafa?

BBC Hausa ta ruwaito cewa maharan haye kan babura sama da 200 sun farwa shingen binciken ababen hawa na Jami'an Kwastam, inda suka ƙona motoci hudu.

Wani da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce harin ya faru da tsakar daren ranar Lahadi, kuma an kashe wani Direban Motar haya amma bai san yadda Fasinjojin motar suka yi ba.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Ƴan Ta'adda Sun Bindige Ango Har Lahira, Sun Sace Amaryarsa Mai Juna Biyu a Kaduna

Hukumar Kwastam da tabbatar da kai harin

Kakakin hukumar Kwastam ta ƙasa reshen Katsina, Isa Danbaba, ya tabbatar da kai harin, inda ya ce maharan sun faramki wurin kan Babura sama da 200.

Ya ce tun farko jami'an da ke Shingen sun samu bayanan sirri game da harin, amma ganin cewa yan ta'addan na da yawa ya sa suka tsere.

"Eh, an kai hari wurin, daga rahoton da muka samu maharan ƙona motocin mu guda biyu da kuma wata Motar hawa ɗaya ta wani Jami'i."

A wani labarin kuma Atiku ya gana da Gwamna Wike bayan lallasa shi a zaɓen fidda gwanin PDP

Atiku Abubakar, ɗan takarar da jam'iyyar PDP ta tsayar a zaɓen shugaban kasa ya gana da gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas a Abuja.

Tsohon mataimakin shugaban ya yi haka ne a wani yunkuri na sulhu da gwamnan, wanda shi ne ya zo na biyu a samun kuri'u.

Kara karanta wannan

Ka taimaka kada ta tayar damu daga gidajenmu: Mazauna garuruwan dake kan titin Abuja-Kaduna

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262