Gagararren mai safarar kwayoyi ya yi kashin kwaya 95 a filin jirgin sama na Abuja

Gagararren mai safarar kwayoyi ya yi kashin kwaya 95 a filin jirgin sama na Abuja

  • Hukumar NDLEA tayi ram da wani mutum dan Najeriya mai shekaru 36 dake zaune a Italy da sunkin kwayar heroin 95 a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja
  • An gano yadda Nwakanma Uche ya hadiyi sunkin miyagun kwayoyi wanda bayan jami'an hukumar sun sa kula da matsinsa ya kasayar
  • Uche wanda 'dan asalin kauyen Arodizuogu na karamar hukumar Ideato na jihar Imo ya bayyana yadda aka yi dashi za a bashi 1.5 miliyan idan ya kai miyagun kwayoyin lafiya Milan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Wani 'dan Najeriya mai shekaru 36 da ke zaune a Italy, Nwakanma Uche, ya kasayar da sunkin kwayar heroin guda 95, bayan jami'an hukumar yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) tayi ram da shi.

An yi ram da Uche ne a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe a Abuja bayan an gano yadda ya hadiyi sunkin, kamar yadda NDLEA ta wallafa a shafinta na Twitter.

Gagararren mai safarar kwayoyi ya yi kashin kwaya 95 a filin jirgin sama na Abuja
Gagararren mai safarar kwayoyi ya yi kashin kwaya 95 a filin jirgin sama na Abuja. Hoto @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

Daraktan watsa labarai na NDLEA, Femi Babafemi ya bayyana hakan a wata takarda da ta fita ranar Lahadi a Abuja.

Babafemi ya labarta yadda aka kama Uche, wanda 'dan asalin kauyen Arodizuogu na karamar hukumar Ideato na jihar Imo, yayin da ya ke kokarin shiga jirgin saman kan hanyarsa zuwa Paris, France da Milan, Italy da ranar Lahadi, 15 ga watan Mayu, 2022.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Saboda haka ne aka kula da motsin shi, ana tsaka da hakan ne ya kasayar da sunkin miyagun kwayoyin 95.
"Ya yi ikirarin cewa ya zo ganin iyayensa a Najeriya bayan kwashe shekaru 12 a Italy.
"Ya kara da cewa, an yi da shi za a biyasa 1.5 miliyan bayan ya kai kwayoyin Milan lafiya," a cewarsa.

NDLEA ta yi ram da mata biyu masu juna 2 dauke da kwayoyi a filin jirgin sama na Legas

A wani labari na daban, hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA), a samame daban-daban, ta kama wasu mata biyu masu juna biyu da wani mai aski da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi.

Kamar yadda takardar da Femi Babafemi, kakakin hukumar ya fitar a Twitter, jami'an hukumar na filin jirgin saman Murtala Muhammad na Legas ne suka yi ram da wadanda ake zargin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel