NDLEA ta yi ram da mata biyu masu juna 2 dauke da kwayoyi a filin jirgin sama na Legas

NDLEA ta yi ram da mata biyu masu juna 2 dauke da kwayoyi a filin jirgin sama na Legas

  • NDLEA tayi ram da mata guda biyu masu juna biyu da wani mai aski da miyagun kwayoyi a filin jirgin saman Murtala Muhammad na Legas
  • An gano yadda Nworie Chikwendu, mai aski ya yi safarar sunkn hodar iblis 44 a takalmansa, tare da bayyana yadda abokinsa ya bashi N2 miliyan a matsayin kudin shigo da ssu
  • An kama daya daga cikin matan 2 da a sunki 7 na miyagun kwayoyi a gwangwanayen giya, yayin da aka kama dayar da tramadol a cikin jaka boye cikin Crayfish

Legas - Hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA), a samame daban-daban, ta kama wasu mata biyu masu juna biyu da wani mai aski da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi.

Kamar yadda takardar da Femi Babafemi, kakakin hukumar ya fitar a Twitter, jami'an hukumar na filin jirgin saman Murtala Muhammad na Legas ne suka yi ram da wadanda ake zargin.

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

NDLEA ta yi ram da mata biyu masu juna 2 dauke da kwayoyi a filin jirgin sama na Legas
NDLEA ta yi ram da mata biyu masu juna 2 dauke da kwayoyi a filin jirgin sama na Legas. Hoto daga 2@ndlea_nigeria
Asali: Twitter

Babafemi ya ce an kama mai askin, Nworie Chikwendu da sunki hudu na hodar iblis boye cikin takalma guda hudu.

Ya ce, wanda ake zargin ya bayyana yadda wani abokinsa ya bashi N2 miliyan a matsayin kudin safarar miyagun kwayoyiin zuwa Najeriya.

"Yayin da aka tsananta bincikar jakarsa, an gano sunki biyu na hodar iblis a takalma kalar ruwan kasa boye a jakar bayansa. A lokacin da aka cigaba da bincikar bakaken takalman da wanda ake zargin ya sanya, an sake gano wasu sunki biyu na hodar iblis karkashin takalmin, hakan yasa gaba daya suka zama sunki hudu masu nauyin 800g," a cewar Babafemi.

A lokacin da aka tuhumi Nworie, wanda yayi ikirarin shi mai aski ne a Sao Paulo, ya ce yazo Najeriya ne don halartar jana'izar mahaifinsa.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya yi murabus daga kujerarsa

Ya fallasa yadda ya yanke hukuncin shiga mummunar sabgar saboda yadda wani abokinsa mai zama a Brazil, ya dauki nauyin tafiyar tasa, gami da bashi miyagun kwayoyin ya kai Legas a kan N2 miliyan.

Kakakin NDLEA Seun Babatunde ya ce, an kama wata mata mai dauke da juna biyu a yankin Iyana na Legas a 4 ga watan Mayu, bayan an kama ta da sunki 7 na kayan maye da gwangwanayen giya.

"An yi hanzarin cafke wacce ta shigo da miyagun ababen daga Dubai, UAE, mai suna shola Ogunrinde, bayan kai samamen, wanda yayi sanadiyyar kama Mrs Seun Babatunde, wacce ke kula da wani gidan giya na Iyana Ipaja," a cewar kakakin hukumar.

Haka zalika, Kakakin NDLEA ya ce, an kama Gloria Asibor, dayar mata mai juna biyun a ranar 5 ga watan Mayu, yayin kokarin tafiya ta jirgin saman kamfanin Turkish da wata jaka dauke da tramadol boye a cikin crayfish.

Kara karanta wannan

Billahil lazi la ilaha illahuwa za mu rike maka amanarka – Gawuna ga Ganduje

A cewarsa, jami'an hukumar sun gano miyagun kwayoyi 300 masu nauyin 200mg da 225mg a jakarta.

NDLEA ta kwace kwayoyin Tramadol na 2.3m, 396Kg na Codeine a Kaduna

A wani labari na daban, hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi ta jihar Kaduna (NDLEA) ta ce jami'anta sun kama kwayoyin tramadol na 2.3 miliyan a cikin jihar.

Mai Jama'a Abdullahi, kakakin rundunar NDLEA ta Kaduna, ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai a ranar Laraba, TheCable ta ruwaito.

A cewar Abdullah, kwayoyin sun kai nauyin 1.2 tonnes, sannan an kama maganin tari na codeine yayin da jami'an hukumar suka kai wani samame a ranar Litinin da Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel