Ana wata ga wata: EFCC ta sake bankado wata badakalar biliyan N90 kan Akanta-Janar, ya zama biliyan N170
- Hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) na kara zurfafa bincike a kan dakataccen Akanta Janar na tarayya, Ahmed Idris
- EFCC ta sake bankado wata badakala ta naira biliyan 90 a kan wanda ke kasa, inda a yanzu jimilar kudi da ake tuhumarsa ya kai naira biliyan 170
- Hakazalika, wata majiya ta hukumar ta ce Akanta Janar din na bayar da hadin kai, don har ya fara ambatan sunayen manyan jami'an gwamnati
Abuja - Binciken da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ke gudanarwa kan dakataccen Akanta-Janar na Tarayya, Ahmed Idris, ya kai naira biliyan 170.
Idris, wanda ke fafutukar neman beli a daren jiya Lahadi, ya magantu kan wasu manyan jami’an gwamnati da ake zargin suna da hannu a wasu hada-hadar kudi.
EFCC ta gano sabbin N90bn da AGF Ahmed Idris ya wawure, ya tona asirin minista da wasu jiga-jigan gwamnati
EFCC ta yiwa wani sakataren din-din-din tambayoyi da ke da alaka da wasu badakaloli da sunansa ya fito a ciki.
Har ila yau, hukumar yaki da rashawar na bibiyar wani minister da aka nunawa yatsa a cikin badakalar na dakataccen Akanta Janar din.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Idan za ku tuna an kama Idris ne bayan ya ki amsa gayyatar da EFCC ta yi masa har sau 80.
A wani bincike da jaridar The Nation ta yi, jami’an EFCC sun gano wasu abubuwa masu ban mamaki game da hada-hadar kudi a ofishin babban Akanta Janar na tarayyar.
An tattaro cewa koda dai da farko ana tuhumar AGF din da badakalar naira biliyan 80 ne, bincike ya gano akwai wata badakalar ta naira biliyan 90.
Akwai alamu da ke nuna cewa AGF din ya yiwa EFCC alkawarin mayar da wasu kudade zuwa asusun gwamnati.
Wata majiya abun dogaro, wacce ta nemi a sakaya sunanta ta ce:
“Zuwa yanzu, shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa da tawagarsa sun samu ci gaba sosai.
“Wannan na daya daga cikin manyan badakaloli da gwamnatin Bawa ta bankado.
“Bisa ga binciken farko, dakataccen AGF din zai yi bayani kan naira biliyan 170. Har yanzu jami’ai na kara zurfafa bincike kan ayyukansa a ofishin.
“Tun bayan da aka kama shi a ranar 16 ga watan Mayu, ya yi wasu bayanai masu amfani ciki harda wasu asusu da ke da ayar tambaya da kuma hada-hadar kudi.”
An tattaro cewa AGF din ya kuma bayyana jerin jami’an gwamnati da ke da hannu a wasu hada-hadar kudi a ofishin nasa.
Majiyar ta kara da cewa:
“Daga cikin abunda ya fadi a yayin binciken, EFCC ta gayyaci wani sakataren din-din-din sannan ta yi masa tambayoyi a makon da ya gabata.
“Sakataren na din-din-din na kan beli yanzu haka kuma an takaita zirga-zirgansa a Abuja. Sakataren ya bayar da wasu jawabai masu amfani a binciken.
“An kuma kira sunan minista a ciki.
“Ya zama dole tantance ko alakanta ministan da aka yi gaskiya ne ko kuma wanda ake zargin yana son shafawa wasu kashin kaza ne.”
Majiyar ta bayar da jawabi kan dalilin da yasa aka bi Idris Kano don kama shi.
“Daga bayanai, hukumar ta gayyaci AGF din sau 80 amma saboda wasu dalilai da shine ya baiwa kansa sani, ya yi biris da bukatar EFCC na tattaunawa da shi. Yana ta guje ma hakan.
“Daga baya an bisa Kano inda aka kama shi a ranar 16 ga Mayu, yana tsare har zuwa jiya amma an bayar da belinsa.
“Akwai bukatar da cike sharuddan beli kuma yana ta fafutukar aikata hakan a ranar Lahadi.”
Da duminsa: EFCC ta yi ram da tsohon gwamna kan zargin hannu a damfarar N80b ta dakataccen AGF
A wani labarin, hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta damke tsohon gwamna Abdulaziz Yari kan binciken da hukumar ke yi game da kudaden da ake zargin akanta janar Ahmed Idris da kwashewa.
Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara, an kama shi ne a yammacin Lahadi a gidansa da ke Abuja, kwanaki kadan bayan da yayi nasarar samun tikitin takarar kujerar sanata na Zamfara ta yamma wanda za a yi a shekara ta gaba. Ya yi nasara babu abokin hamayya, Premium Times ta ruwaito.
Asali: Legit.ng