EFCC ta gano sabbin N90bn da AGF Ahmed Idris ya wawure, ya tona asirin minista da wasu jiga-jigan gwamnati
- Hukumar EFCC ta sake binciko wasu sabbin N90 biliyan bayan N80 biliyan da ake zargin AGF Ahmed Idris da handama, jimilla ta kai N170 biliyan a yanzu
- A yayin bincikarsa, Idris ya bayyana sunan wani minista tare da wasu manyan jami'an gwamnati da ke da hannu wurin damfarar N170 biliyan
- An gano cewa, Idris yana bada hadin kai wurin binciken inda a halin yanzu har an gayyaci wani sakataren gwamnatin tarayya da Idris ya ambata
- Majiya ta sanar da cewa, Idris ya sha alwashin mayar da wasu tsabar kudi zuwa lalitar gwamnati yayin da ya ke rokon EFCC da ta bada belinsa
Abuja - Bincike kan makuden kudaden da hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, game da dakataccen akanta janar na tarayya, Ahmed Idris, ya haura ya kai N170 biliyan, rahoton jaridar The Nation ya bayyana.
Idris, wanda a daren jiya ya ke neman a bada belinsa, ya bayyana sunayen wasu manyan jami'an gwamnati da ke da hannu cikin handamar kudaden kasar da ake tuhumarsa a kai.
Hukumar EFCC ta tuhumi wani babban sakataren gwamnati kan wasu daga cikin kudaden da ake zarginsa da rub da ciki a kai.
A halin yanzu, hukuma tana cigaba da sanya ido kan wani minista wanda dakataccen akanta janar din ya ambaci sunansa a harkallar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gano cewa, hukumar EFCC ta damke Ahmed Idris ne bayan ya yi watsi da gayyata 80 da ta aike masa da ita.
Kamar yadda binciken jaridar The Nation ya bayyana, jami'an EFCC sun bankado wasu manyan almundahanar kudade daga ofishin akanta janar din.
An tattaro cewa, duk da a farko ana zargin AGF din da wawurar kudade har N80 biliyan, bincike ya nuna cewa akwai karin wasu N90 biliyan.
Kisan gillan da IPOB suka yiwa Bahaushiya da 'ya'yanta 4: Gwamnan Anambra ya ce ba Hausawa aka nufi farmaka ba
Akwai alamu da ke nuna cewa, AGF din ya bai wa hukumar EFCC hadin kai inda ya yi alkawarin mayar da wasu tsabar kudi zuwa lalitar gwamnatin.
Majiya mai karfi wacce ta bukaci a boye sunanta ta ce: "A halin yanzu dai, shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa da tawagarsa sun samu matukar cigaba a wannan binciken.
"Wannan yana daya daga cikin manyan almundahana da mulkin Bawa a EFCC ta bankado.
"Hadi da binciken farko, dakataccen AGF din a halin yanzu zai bayyana inda N170 biliyan ta shiga ne. Har yanzu jami'ai suna cigaba da bincike kan al'amuran ofishinsa.
"Tun bayan kama shi a ranar 16 ga watan Mayu, ya yi wasu fallasa da suka hada da wasu asusun bankuna da harkallar kudade masu ayoyin tambaya."
An tattaro cewa, dakataccen AGF din ya bayar da jerin sunayen jami'an gwamnati da ke da alaka da wasu al'amuran kudade a ofishinsa yayin da ya ke akanta janar.
Majiyar ta ce: "Daga cikin fallasarsa yayin binciken, an gayyaci wani babban sakateren gwamnatin tarayya kuma EFCC ta tuhume shi a makon da ya gabata.
"A halin yanzu an bayar da belin babban sakataren kuma an kayyade yawonsa da iyakar Abuja kadai. Babban sakataren ya bada wasu muhimman bayanai ga masu binciken.
"An bayyana sunan wani minista a ciki. Mun tantance ko akwai alakar lamarin da ministan ko kuma kawai wanda ake zargi ya shirya labaransa ne."
EFCC ta yi ram da tsohon gwamna kan zargin hannu a damfarar N80b ta dakataccen AGF
A wani labari na daban, hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta damke tsohon gwamna Abdulaziz Yari kan binciken da hukumar ke yi game da kudaden da ake zargin akanta janar Ahmed Idris da kwashewa.
Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara, an kama shi ne a yammacin Lahadi a gidansa da ke Abuja, kwanaki kadan bayan da yayi nasarar samun tikitin takarar kujerar sanata na Zamfara ta yamma wanda za a yi a shekara ta gaba. Ya yi nasara babu abokin hamayya, Premium Times ta ruwaito.
Asali: Legit.ng