Mutum 31 Suka Mutu Yayin Turereniya Wurin Taron Rabon Abinci Da Coci Ta Shirya a Rivers, 'Yan Sanda

Mutum 31 Suka Mutu Yayin Turereniya Wurin Taron Rabon Abinci Da Coci Ta Shirya a Rivers, 'Yan Sanda

  • Mutane 31 sun rasu yayin wata turereniya da aka yi a wani cocin Kings Assembly a Port Harcourt, Jihar Rivers a safiyar yau Asabar 28 ga watan Mayu
  • Mutanen sun zo halartar wani bikin rabon kayan abinci ne da cocin da shirya yi amma kafin fara taron wasu suka bude wani karamin kofa kuma aka rika turereniya wurin kutsawa
  • Mukadashiyar kakakin yan sandan Rivers, Grace Iringe Koko ta tabbatar da afkuwar lamarin tana maicewa an fara sahihin bincike domin kara sanin musababbin afuwar lamarin

Rivers - Rundunar yan sandan Jihar Rivers ta ce mutane 31 ne suka mutu a turereniyar da aka yi wurin wani taron rabon kyaututuka da kayan abinci a coci da ke Port Harcourt, safiyar ranar Asabar, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Fasto: A coci aka tara buhunnan kudi domin biyan 'yan bindigan da suka sace ni

Cocin, mai suna Kings Assembly ya gayyaci mambobi ne domin hallartar wani biki inda aka yi alkawari rabon kyautuka da kayan abinci.

Mutum 31 Suka Mutu Yayin Turereniya Wurin Taron Rabon Abinci Da Coci Ta Shirya a Rivers, 'Yan Sanda
'Yan Sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutum 31 a Wurin Rabon Abinci Da Coci Ta Shirya. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

Cocin yana kusa da GRA ne a Port Harcourt amma an shirya yin taron ne a Polo Club na Port Harcourt, saboda ana tsammin mutanen da dama za su hallara.

Mukadashiyar kakakin yan sandan Rivers, Grace Iringe Koko ta tabbatar mutum 31 sun rasu, tana mai cewa cocin ta shirya taron ne don raba wa mutane kayan tallafi amma sai abin ya auku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mutum 31 suka rasu. Turereniya aka yi saboda cocin ta yi alkawarin raba wa mutane kayan abinci.
"Ana daf da fara taron. Karfe 9 na safe ya kamata a fara. Amma wasu mutane sun isa wurin kafin lokacin kuma suka kutsa suka shiga ciki.
"Don haka aka fara turereniya.
"Bayanan da muka samu ya nuna cocin na son tallafawa gajiyayyu ne da kayan abinci da wasu kyaututtuka.

Kara karanta wannan

2023: Duk da nukun-nukun da ake yi, akwai yiwuwar APC ta tantance Jonathan a yau

"Amma an fara bincike don gano ainihin dalilin afkuwar lamarin," in ji SP Iringe-Koko.

Tunda farko kun ji cewa Daily Trust ta rahoto cewa wani shaidan gani da ido, ya ce lamarin ya faru ne yayin bikin rabon kyauta da kayan abinci karo na hudu da cocin ta yi.

Wani da abin ya faru a gabansa ya magantu

Shaidan ya ce wasu cikin bakin sun iso tun ranar Juma'a yayin da wasu suka iso misalin karfe 6.30 na safiyar ranar Asabar don taron da aka shirya farawa karfe 9 na safe.

Shaidan ya ce wasu mutane da za su yi wasannin motsa jiki sun iso haraban cocin misalin karfe 8 na safe kuma suka bude wani karamin kofa, hakan ya bawa dandazon mutanen da ke waje damar kutsawa cocin, hakan ya janyo turereniyar.

"A yau da safe abin ya faru. Cocin ya gayyaci mutane wurin bikin rabon kyauta da kayan abinci karo na hudu. Wasu sun taho tun ranar Juma'a, wasu kuma suka iso tun karfe 6.30 na ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Nakiya ta sake tashi a gidan giya yayinda yan PDP ke murnar nasarar Atiku

"Wasu da za su yi wasannin motsa jiki sun bude wata karamar kofa sai dandazon mutanen da ke waje suka kutsa kai kuma aka yi turereniya. Na kirga kimanin gawa 21 a kasa," in ji shi.

Ya ce an garzaya da mutane da dama zuwa wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba.

Hakazalika, Legit.ng ta samu karin bayani ta bakin wata 'yar kasuwa mazauniyar Port Harcourt wacce ta nemi a sakaya sunanta saboda tsaro.

Ta jadada cewa sunan malamin cocin Fasto Chris Ugoh kuma dama ya saba irin wannan sadaka na kayayyaki da abinci shekaru uku da suka gabata, wannan karon ne na hudu.

Ta kara da cewa ta samu labarin cewa wasu mutane biyu sun kara rasuwa cikin wadanda aka kai asibiti jinya.

Ta kuma ce cikin wadanda suka rasu a ranar farkon akwai wata mata da 'ya'yanta uku kuma dukkansu sun riga mu gidan gaskiya.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Wani abu mai fashewa ya sake tashi a wata jihar arewacin Najeriya

"Matar sun rabu da mijinta ya bar ta da yara uku don haka tana cikin bukata. Tana cikin wadanda suka rasu yayin turereniyar da aka yi a cocin.
"Wasu karin mutane bayan 31 na farkon sun kara rasuwa," in ji ta.

'Batanci: Ba Za Mu Lamunci Kashe Kiristoci a Bauchi Ba Da Sunan Zagin Annabi, CAN Ta Ja Kunnen Musulmi

A wani rahoton, Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta nuna bacin ranta dangane da zargin wata da batanci da aka yi a Jihar Bauchi, inda ta ja kunne akan cewa ba za ta lamunci kisa da sunan batanci ba, Leadership ta ruwaito.

Kungiyar ta CAN kalubalanci gwamnati da kuma jami’an tsaro akan su yi gaggawar daukar matakin da ya dace akan tozarta kundin tsarin mulkin da ake yi kafin gagarumin tashin hankali ya barke wanda za a kasa dakatar da shi.

A wata takarda wacce shugaban kungiyar na reshen Jihar Kaduna, Rabaran Joseph John Hayab ya saki, ya ce CAN ta kula da yada ake amfani da sunan batanci a arewacin Najeriya ana halaka wadanda ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ba su karasa halakawa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: