Tashin hankali: Sojoji sun kashe sufeto na 'yan sanda da duka a Najeriya

Tashin hankali: Sojoji sun kashe sufeto na 'yan sanda da duka a Najeriya

- An zargi wasu sojoji dake gadin wani kamfani a jihar Ribas da laifin kashe wani dan sanda

- Hakan ya biyo bayan wani rahoto da jaridar PUNCH ta fitar, inda ta bayyana cewa tayi hira da daya daga cikin 'yan uwan dan sandan

- Sai dai kuma ya bayyana cewa har ya zuwa yanzu babu wanda ya fito yayi magana akan kisan dan uwan nasa

Rundunar 'yan sandan jihar Ribas ta bayyana sufeton ta da take zargin sojoji sun kashe da duka a jihar.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, Nnamdi Omoni, ya bayyana jami'in dan sandan da suna Hosea Yakubu, inda ya kara da cewa har yanzu suna cigaba da bincike akan lamarin.

Tashin hankali: Sojoji sun kashe sufeto na 'yan sanda da duka a Najeriya
Tashin hankali: Sojoji sun kashe sufeto na 'yan sanda da duka a Najeriya
Asali: Facebook

An gano cewa wasu sojoji dake gadin wani kamfani ne suka kashe wannan dan sanda bayan ya karya dokar bin hanya a gaban kamfanin a ranar Lahadi 16 ga watan Agusta, 2020.

Dan uwan wannan jami'in dan sanda da yayi hira da PUNCH akan wannan aika-aika ya bukaci a boye sunansa, inda ya ce: "Dan uwana tare da 'yan sanda guda biyu sun ki bin dokar hanya sakamakon shinge da aka sanya a gaban kamfanin na Eleme Petrochemical, sai wani soja ya tsare su, musu yayi nisa har ya zama fada. Daya daga cikin sojojin wanda ya shiga fadan yayi amfani da katon falanki ya makawa dan uwana a kai, take ya fadi ya daina motsi.

"Cikin gaggawa aka garzaya dashi asibiti don ceto rayuwar shi.

KU KARANTA: Mutum uku sun rasa rayukansu, yayin da aka kone gidaje masu yawan gaske a wani sabon rikici da ya barke tsakanin kabilar Tiv da Jukun

"Bayan shafe awa 24 a asibiti, sai ya mutu. Har yanzu daga 'yan sandan har sojojin babu wanda yayi magana akan wannan lamari ko ya dauki mataki a kai."

Da aka tuntubi kakakin rundunar sojin dake Fatakwal, Charles Ekeocha, ya ce bashi da labari akan wannan lamari, amma yayi alkawarin bayyana labarin da zarar ya samu labari akan lamari. Amma dai har ya zuwa lokacin da muka rubuta wannan rahoto bai ce komai ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel