Harkallar Kwaya: Bayan tsallake kisa a magarkama, Kyari da abokansa sun bayyana a kotu

Harkallar Kwaya: Bayan tsallake kisa a magarkama, Kyari da abokansa sun bayyana a kotu

  • Yanzu muke samun labarin cewa, an sake gurfanar da Abba Kyari a gaban kotun Abuja bisa zargin harkallar kwaya
  • Wannan na zuwa ne awanni bayan samun rahotannin da ke cewa, wasu sun kitsa illata shi a magarkamar da yake ajiye
  • Ya zuwa yanzu, Abba Kyari bai amsa laifukan da ake tuhumarsa da su ba, amma wasu biyu daga tawagarsa sun amsa

Abuja - An sake kawo dakataccen dan sanda Abba Kyari tare da wasu mutane shida kotu domin amsa laifukan safarar miyagun kwayoyi da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta ke zarginsu dashi.

Hukumar ta NDLEA ta shigar da laifuka takwas da suka hada da safarar miyagun kwayoyi kan Abba Kyari, wanda kuma ke ci gaba da fuskantar shari'a a Amurka saboda alakarsa da dan damfarar yanar gizo, Ramon ‘Hushpuppi’ Abbas.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace malamin addini da wasu mutane 7 a jihar Katsina

Kyari da tawagarsa suin gurfana a gaban kotu
Harkallar Kyari: Bayan tsallake kisa a magarkama, Abba Kyari da abokansa sun ayyana a kotu | Hoto: thecable.ng
Asali: Facebook

Wadanda aka gurfanar tare da Kyari sun hada da ACP Sunday Ubua, ASP Bawa James, Insfekta Simon Agirigba, Insfekta John Nuhu, Chibuinna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne.

A cewar rahoton Channels Tv, Kyari, kafin dakatar da shi, tsohon mataimakin kwamishinan ‘yan sanda ne da ke jagorantar tawagar nan ta 'yan sandan IRT da aka rushe.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tun da farko dai Abba Kyari ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, sai dai biyu daga cikin wadanda ake tuhumarsu tare sun amsa laifin da ake zarginsu; safarar miyagun kwayoyi.

Wadanda suka amsa laifin; Chibuinna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne, sun gabatar da rokonsu a babbar kotun tarayya da ke Abuja na neman sassauci.

Dukkan mutanen biyu, an bayar da umarnin a ci gaba da tsare su a hannun hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) har sai lokacin da za a saurari bukatar neman belinsu.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Tashin hankali yayin da PDP ta dage zaben fidda gwani bayan barkewar rikici

A baya dai an ki amincewa da neman belin Kyari, kuma yayin da bincike ya tsananta, hukumar ta NDLEA ta samu nasarar cafke wani mutum da ake zargin hamshakin attajiri ne da ke bayan harkallar ta Kyari.

Abba Kyari ya sha da kyar, saura kiris masu fushi da shi su hallaka shi a gidan yari

A wani labarin, jami'an gidan yari suna tunanin mayar da jami'in 'dan sanda Abba Kyari daga gidan yarin Kuje zuwa hannun jami'an tsarin farin kaya bayan wasu daga cikin abokan zamansa sun yi yunkurin halakasa sakamakon zarginsa da rashin gaskiya wajen bada cin hanci don a samar musu da kwangila a lokacin da yake kan aiki.

Kamar yadda wasu takardun cikin gida da Premium Times ta samu damar gani suka bayyana, an kai masa harin ne a 4 ga watan Mayu, watanni bayan kama Kyari da laifin safarar miyagun kwayoyi. Maharansa sun kai kimanin 190, a cewar wani jami'i, kuma da yawansu an kai su gidan yarin ne saboda harkallar miyagun kwayoyi.

Kara karanta wannan

Daga korafi a Facebook: Mutumin da gwamnan APC ya daure saboda sukar gwamnatinsa ya kubuta

Kyari, mai shekaru 47, mataimakin kwamishinan 'yan sanda, wanda jami'in tsaro ne sannan hazikin kungiyar binciken sirri na sifeta-janar kafin ya kwafsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.