Harin jirgin Abuja-Kaduna: Sulhu kadai ne mafita wajen ceto sauran fasinjojin, Wacce yan bindigan suka saki
- Kwanakin baya, yan ta'addan Ansaru da suka kai harin Bam jirgin kasan Abuja-Kaduna kuma suka debi fasinjoji sun saki mace daya mai juna biyu bisa tausayi
- A hirar da tayi bayan samun kubuta, ta yi kira ga gwamnatin tarayya tayi gaggawan sulhu da wadannan mutane saboda shine mafita daya tilo
- Thamina ta yi bayanin abubuwan da idanuwanta suka gani yayinda take hannun yan bindigan
Kaduna - Thamina Mahmood na daya daga cikin mutum 62 da yan ta'addan suka sace a harin da suka kai jirgin kasan Abuja-Kaduna ranar 28 ga watan Maris, 2022.
Thamina, wacce ke dauke da juna biyu ta samu kubuta saboda halin da take ciki kuma ta bayyana abubuwan da suka faru.
Harin jirgin kasan Abj-Kad: An nemo 'ya'ya 8 na 'yan ta'adda, ana shirin mika musu don fansar fasinjoji
A hirarta da Daily Trust, ta yi bayanin cewa sulhu kadai ne mafita wajen ceto sauran wadanda ke hannun yan bindigan.
Tace:
"Sun fadi abinda suke bukata daga wajen gwamnati. Shi yasa suka yi amfani da mu wajen janyo ra'ayin gwamnati don ta basu abinda suke so."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Abinda suke so shine gwamnati ta sako 'yayansu. Sunce yadda suka ji tausayi na, ita ma gwamnati ta sauraresu ta sake musu 'yayansu da sauran jama'arsu."
Yayinda aka tambayeta shin sun yi alkawarin sakin wadanda ke hannunsu idan gwamnati ta saki 'yayansu? tace:
"Sun ce 'yayansu na hannun gwamnati kuma idan aka sakesu, zasu saki namu 'yayan da kuma wasu gajiyayyu dake hannunsu. Sannan su tattauna kan sauran."
Labarin haihuwar Thamina a hannun yan bindiga
Kwanakin baya kafafen yada labarai sun ruwaito cewa Thamina ta haihu a hannun yan bindiga, amma yanzu tace ba gaskiya bane.
Tace:
"Yadda kuka ji nima haka naji; na kusa haihuwa dai yanzu, lokaci ya kusanto."
Ku saki 'yayanmu 8 dake hannunku a Yola sai mu saki fasinjojin jirgin kasan Abuja: Yan ta'addan
Yan ta'addan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna sun yi barazanar fara kashe wadanda suka kwashe idan gwamnatin tarayya bata saki yaransy dake hannunta ba.
Shugaban yan ta'addan, Abu Barrah, yace gwamnati ta ajiye 'yayansu a gidan marayu dake Yola.
Abu Barrah ya bayyana hakan ne ga Tukur Mamu, shugaban kamfanin jaridan Desert Herald.
Asali: Legit.ng