Da Duminsa: Yan bindiga sun kashe Soja, sun sace wani ɗan ƙasar waje a Ondo

Da Duminsa: Yan bindiga sun kashe Soja, sun sace wani ɗan ƙasar waje a Ondo

  • Wasu yan bindiga sun sace wani Injiniya ɗan ƙasar Lebanon a yankin garin Owo da ke jihar Ondo ranar Laraba
  • Wani shaida da abun ya faru a gabansa ya ce maharan sun kashe wani soja da ke ba shi tsaro da kuma direban da ke tuƙa shi
  • Kakakin yan sandan Ondo, SP Fumilayo Odunlami, ya ce suna cigaba da binciken ceto mutumin da aka sace da cafke maharan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ondo - Wasu miyagun yan bindiga da ba'a gane ko su waye ba sun halaka sojan Najeriya guda ɗaya kuma suka yi awon gaba da wani ɗan kasar waje a garin Owo da ke ƙaramar hukumar Owo jihar Ondo.

Wata majiya daga cikin jami'an tsaro ta bayyana cewa mutumin da suka sace ya kasance ɗan kwangila da ke aiki a yankin, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jirgin da aka gani a titin Legas ba hadari yayi ba, sayarwa wani akayi yake kokarin kaishi gida: FAAN

Matsalar rashin tsaro a Najeriya.
Da Duminsa: Yan bindiga sun kashe Soja, sun sace wani ɗan ƙasar waje a Ondo Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A cewar majiyar ɗan kwangilar ya na aiki ne a ɗaya daga cikin ayyukan da gwamnatin jihar Ondo ke gudanarwa a yankin Owo.

Kazalika, majiyar wacce ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce maharan sun aikata haka ne a yankin da ke kusa da cibiyar lafiya ta tarayya (FMC) ranar Laraba da yamma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani shaidan gani da ido ya ce maharan sun halaka direban mutumin, wanda ɗan asalin ƙasar Lebanon ne yayin harin.

Jaridar The Nation ta rahoto shedan ya ce:

"Maharan sun sace ɗan ƙasar wajen wanda muke kira da Farin Injiniya, sun kashe dirabansa da kuma wani soja da ke aikin ba shi tsaro. Yan bindigan sun buɗe wuta sosai a cikin iska."

Bayanai sun nuna cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin ranar Laraba, 25 ga watan Mayu, shekarar 2022.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jami'an tsaro sun budewa magoya bayan Okorocha wuta a farfajiyar gidansa

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Ondo, SP Fumilayo Odunlami, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce hukumar yan sanda na cigaba da kokarin ceto wanda maharan suka sace.

A wani labarin kuma Sarki ya tsige wani Dagaci bayan gano yana da hannu a aikata wani laifi a jihar Kano

Mai Martaba Sarkin Gaya a jihar Kano, Aliyu Ibrahim Abdulƙadir, ya tube rawanin magajin garin Gudduba da ke yankin Ajingi.

A cewar sarkin bayan dogon lokaci ana gudanar da bincike an gano cewa basaraken na da hannu a cutar talakawa filaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262