Jirgin da aka gani a titin Legas ba hadari yayi ba, sayarwa wani akayi yake kokarin kaishi gida: FAAN

Jirgin da aka gani a titin Legas ba hadari yayi ba, sayarwa wani akayi yake kokarin kaishi gida: FAAN

  • Hukumar FAAN ta saki jawabin kar ta kwana kan jirgin da aka gani an titi a jihar Legas da daren Talata
  • FAAN ta karyata labarin cewa jirgin hadari yayi ya fado tsakiyar jama'a, tace na sayarwa ne
  • Wani mutumi ne ya sayi jirgin amma a lalace, shine yake kokarin kaishi wajen gyara

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ikeja, Legas - Hukumar jiragen saman Najeriya (FAAN) ta yi watsi da rahotannin cewa wani jirgin sama ya yi hadari a Ikeja, babbar birnin jihar Legas ranar Talata.

Hotuna da bidiyoyi sun nuna yadda aka ga jirgin saman tsakiyar titi ranar Talata wanda ya haddasa cinkoson motoci.

hUkumar FAAN
Jirgin da aka gani a titin Legas ba hadari yayi ba, sayarwa wani akayi yake kokarin kaishi gida: FAAN Hoto: @DarkAmoke
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amma a jawabin da hukumar ta fitar da daren talatan, ta bayyana cewa jirgin da aka gani a titi ba hadari yayi ba, ya lalace ne kuma aka sayarwa wani yana kokarin kaita matsuguna.

Kara karanta wannan

Gagararren mai safarar kwayoyi ya yi kashin kwaya 95 a filin jirgin sama na Abuja

A cewar jawabin:

"Hukumar jiragen saman Najeriya na amfani da wannan dama wajen sanarwa daukacin yan Najeriya cewa suyi watsi da rahotatannin dake yawo a kafafen ra'ayi sada zumunta kan hadarin jirgi a Ikeja."
"Mai jirgin ne ya siyarwa wani shi kuma yake kokarin kaita inda zai ajiye."

Kalli bidiyon jirgin:

Gagararren mai safarar kwayoyi ya yi kashin kwaya 95 a filin jirgin sama na Abuja

Wani 'dan Najeriya mai shekaru 36 da ke zaune a Italy, Nwakanma Uche, ya kasayar da sunkin wiwi guda 95, bayan jami'an hukumar yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) tayi ram da shi.

An yi ram da Uche ne a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe a Abuja bayan an gano yadda ya hadiyi sunkin, kamar yadda NDLEA ta wallafa a shafinta na Twitter.

Daraktan watsa labarai na NDLEA, Femi Babafemi ya bayyana hakan a wata takarda da ta fita ranar Lahadi a Abuja.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: EFCC ta sake bankado wata badakalar biliyan N90 kan Akanta-Janar, ya zama biliyan N170

Babafemi ya labarta yadda aka kama Uche, wanda 'dan asalin kauyen Arodizuogu na karamar hukumar Ideato na jihar Imo, yayin da ya ke kokarin shiga jirgin saman kan hanyarsa zuwa Paris, France da Milan, Italy da ranar Lahadi, 15 ga watan Mayu, 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel