Kano: Sarki ya tsige wani Dagaci bayan gano yana da hannu a aikata wani laifi
- Mai Martaba Sarkin Gaya a jihar Kano, Aliyu Ibrahim Abdulƙadir, ya tube rawanin magajin garin Gudduba da ke yankin Ajingi
- A cewar sarkin bayan dogon lokaci ana gudanar da bincike an gano cewa basaraken na da hannu a cutar talakawa filaye
- Sarkin ya gargaɗi Sarakunan gargajiya da sauran naɗe-naɗen Sarauta da su guji ba ta wa masarauta suna a idon talakawanta
Kano - Masarautar Gaya da ke jihar Kano ta tube rawanin Dagacin Gudduba, Mallam Usman Muhd Lawan, da ke yankin karamar hukumar Ajingi a Kano.
Mai Martaba Sarkin Gaya, Dakta Aliyu Ibrahim Abdulkadir, shi ne ya sanar da haka kuma ya ce matakin zai fara aiki ne nan take, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Sarkin ya ce bayan tsayin lokaci ana gudanar da bincike ta tabbata Basaraken ya na da hannu dumu-dumu a damfara da cutar mutane filaye.
Bisa haka Masarautar Gaya ta umarci Hakimin karamar hukumar Ajingi, Alhaji Wada Aliyu, (Madakin Gaya), ya tura wakilan masarautarsa domin su kula da harkokin kauyen.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ba zamu yarda a ɓata mana suna ba - Sarkin Gaya
Sarkin na Gaya ya kara da gargaɗin cewa, "Masarautarsa ba zata lamurci duk wani rashin ɗa'a da ka iya ruguza kyakkyawan kallon da al'umma ke mata ba."
Haka zalika, ya shawarci dukkan sarakunan gargajiya da ke ƙarƙashin masarautar Gaya da su sanya gaskiya wajen sauke nauyin da Allah ya ɗora mu su.
Bayan haka ya yi kira ga mutanen da aka naɗa wa rawanin wata Sarauta su natsu su martaba yardar da Masarauta ta musu.
A wani labarin na daban kuma Mataimakin Tambuwal da wasu mutum huɗu sun janye daga takara, tsohon Minista ya fice daga PDP
A jawabin shugaban kwamitin zaɓen fidda gwanin PDP a Sokoto ya sanar da sunayen mutum biyar da suka janye daga takara.
Ya ce mataimakin gwamna Tambuwa l, shugaban PD P na jiha da wasu mutum uku sun janye daga shiga zaɓen.
Asali: Legit.ng