Hawaye sun kwaranya yayin da aka binne Bahaushiyar da IPOB suka kashe da yaranta 4 a Anambra
- An binne Harira Jubril da yaranta hudu da yan haramtacciyar kungiyar IPOB suka kashe a jihar Anambra a ranar Laraba, 25 ga watan Mayu
- Mijinta, Jubril Ahmed ya ce ya canja shawarar binne su a Anambra ne saboda gawawwakinsu sun bara rubewa tunda ba a saka su a dakin ajiye gawa ba
- Ya kuma bayyana cewa tuni ya tattara yanasa-yanasa zai koma mahaifarsa ta jihar Adamawa don fara sabuwar rayuwa tunda an shafe iyalinsa gaba daya
Anambra - An yi jana'izar Harira Jubril, mata mai ciki da yan awaren IPOB suka yiwa kisan gilla tare da yaranta hudu a jihar Anambra a ranar Laraba, 25 ga watan Mayu.
Daily Trust ta rahoto cewa an binne marigayiya Harira da yaranta Fatima mai shekaru 9, Khadijah mai shekaru 7; Hadiza mai shekaru 5 da Zaituna mai shekaru 2 cike da hawaye.
Mijin marigayiyar, Jubril Ahmed, ya fada ma jaridar Daily Trust cewa ya canja ra’ayinsa na daukar gawawwakinsu zuwa mahaifarsa a jihar Adamawa saboda ba a saka su a dakin ajiyar gawa ba kuma sun fara rubewa.
Sai dai kuma, ya bayyana cewa zai koma Adamawa domin sake sabuwar rayuwa tunda haramtacciyar kungiyar ta shafe iyalinsa gaba daya daga doron kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
“A yanzu haka da nake maku magana, ina a hanyata ta zuwa jihar Adamawa mahaifata kuma zan koma chan da zama gaba daya don fara sabuwar rayuwa a chan, tunda sun shafe iyalina gaba daya.
“Gwamnan jihar Anambra, Chukwuma Charles Soludo, ya tallafa mun da N500,000 kuma na godema abokaina da yan uwa da suka bani gudunmawa tunda abun ya faru.”
Da yake amsa wata tambaya, Jubril ya ce:
“Daukacin al’ummar arewa sun bar yankin saboda tsoron rayuwarsu na cikin hatsari, duk sun koma gida; yayin da sauran ke a hanyarsu ta komawa gida.”
Anambra: Bayan kisan yar Arewa da 'ya'yanta 4, gwamna ya fara taka wa IPOB birki
A wani labarin, gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya kafa dokar ta-baci fita a kananan hukumomi bakwai na jihar domin daukar mataki kan ayyukan IPOB ke yi.
Yankunan da abin ya shafa sun hada da Aguata, Ihiala, Ekwusigo, Nnewi ta Arewa, Nnewi ta Kudu, Orumba ta Arewa da Orumba ta Kudu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi a jihar a ranar Laraba, 25 ga watan Mayu.
Asali: Legit.ng