Anambra: Bayan kisan yar Arewa da 'ya'yanta 4, gwamna ya fara taka wa IPOB birki

Anambra: Bayan kisan yar Arewa da 'ya'yanta 4, gwamna ya fara taka wa IPOB birki

  • Gwamna Soludo, a ranar Laraba ya yi jawabi ga al’ummar jihar Anambra tare da kafa dokar ta-baci a kananan hukumomi bakwai na jihar
  • A cewar Soludo, dokar ta-bacin za ta fara aiki ne a ranar Juma’a 26 ga Mayu, 2022, a yankuna kamar su Aguata, Ihiala, Ekwusigo, Nnewi ta Arewa, Nnewi ta Kudu, Orumba ta Arewa da Orumba ta Kudu
  • Gwamnan jihar Anambra ya kuma yi kira ga mazauna yankunan da abin ya shafa da su hada hannu da gwamnati a wannan umarni

Jihar Anambra - Wani rahoto da jaridar Daily Trust ta fitar ya ce, gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya kafa dokar ta-baci fita a kananan hukumomi bakwai na jihar domin daukar mataki kan ayyukan IPOB ke yi.

Kara karanta wannan

Zaben Fidda Gwanin PDP: Bidiyon Ƙanen Fayose Suna Tiƙa Rawa Da Waƙar Zolayar Dino Melaye

Yankunan da abin ya shafa sun hada da Aguata, Ihiala, Ekwusigo, Nnewi ta Arewa, Nnewi ta Kudu, Orumba ta Arewa da Orumba ta Kudu.

Gwamnan Anambra ya fara daukar mataki kan harin IPOB
Anambra: Bayan kashe 'yar Arewa da 'ya'yanta, gwamna ya fara daukar mataki kan IPOB | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi a jihar a ranar Laraba, 25 ga watan Mayu.

Yadda dokar ta-bacin take

Ya ce dokar ta-bacin za ta fara aiki ne daga ranar Juma’a 26 ga watan Mayu, za ta yi aiki har sai an dawo da zaman lafiya a yankunan da lamarin ya shafa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Soludo ya ce:

“Daga gobe Juma’a, 26 ga Mayu, 2022, dokar ta-baci daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe ta ta fara aiki kan babura (okada), keke napep (keke), da motocin bas a Aguata, Ihiala, Ekwusigo, Nnewi ta Arewa, Nnewi ta Kudu, Ogbaru, Kananan Hukumomin Orumba ta Arewa da Orumba ta Kudu har sai an sanar da sabon batu.”

Kara karanta wannan

Rayuwar dan Adam ta yi arha a Najeriya: CAN ta yi Alla-wadai da kisan Fatima da yaranta a Anambra

“Har ila yau, an hana babura, keke napep da motocin bas yin aiki a cikin wadannan kananan hukumomin a ranakun Litini har sai lokacin da dokar zaman gida ta tsaya gaba daya."

Kisan gillan da IPOB suka yiwa Bahaushiya da 'ya'yanta 4: Gwamnan Anambra ya ce ba Hausawa aka nufi farmaka ba

A wani labarin, gwamna Chukwuma Soludo na jihar Anambra ya bayyana cewa ba yan arewa ake nufin kashewa ba a jihar.

Soludo ya bayyana hakan ne yayin da yake martani ga kisan wata mata mai ciki da yaranta da wasu da ake zaton yan awaren IPOB ne suka yi, Daily Trust ta rahoto.

A cikin wata sanarwa daga Mista Christian Aburime, babban sakataren labaransam Soludo ya ce yan asalin Anambra, yan arewa da mutane daga sauran yankunan kasar suna zama tare da yin kasuwanci da juna cikin lumana, rahoton Daily Post.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.