Kisan gillan da IPOB suka yiwa Bahaushiya da 'ya'yanta 4: Gwamnan Anambra ya ce ba Hausawa aka nufi farmaka ba

Kisan gillan da IPOB suka yiwa Bahaushiya da 'ya'yanta 4: Gwamnan Anambra ya ce ba Hausawa aka nufi farmaka ba

  • Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya yi martani a kan kisan wata yar arewa mai ciki da yaranta hudu da yan IPOB suka yi
  • Farfesa Soludo ya bayyana cewa sabanin yadda ake yayatawa, ba yan arewa ake nufin kashewa ba a jihar
  • Ya kuma ba da tabbacin samar da cikakken kariya da tsaro ga al'ummar Hausawa da ma mazauna jihar gaba daya

Anambra - Gwamna Chukwuma Soludo na jihar Anambra ya bayyana cewa ba yan arewa ake nufin kashewa ba a jihar.

Soludo ya bayyana hakan ne yayin da yake martani ga kisan wata mata mai ciki da yaranta da wasu da ake zaton yan awaren IPOB ne suka yi, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

An ki cin biri, an ci dila: Yadda sabon AGF ke da jikakkiyar tuhumar rashawa da EFCC

Kisan gillan da IPOB suka yiwa Bahaushiya da 'ya'yanta 4: Gwamnan Anambra ya ce ba Hausawa aka nufi farmaka ba
Kisan gillan da IPOB suka yiwa Bahaushiya da 'ya'yanta 4: Gwamnan Anambra ya ce ba Hausawa aka nufi farmaka ba Hoto: The Cable
Asali: UGC

A cikin wata sanarwa daga Mista Christian Aburime, babban sakataren labaransam Soludo ya ce yan asalin Anambra, yan arewa da mutane daga sauran yankunan kasar suna zama tare da yin kasuwanci da juna cikin lumana, rahoton Daily Post.

Jawabin ya kuma bayyana cewa gwamnatin Soludo ta nuna jajircewa wajen magance rashin tsaro, sannan kuma tana ci gaba da ba yan gari da baki a jihar tabbacin samun kariya da tsaro.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A halin da ake ciki, kwamishinan yan sandan jihar Anambra, Echeng E. Echeng, ya ziyarci al’ummar Hausawa a jihar sannan ya basu tabbacin samun kariya.

Yayin da yake ba mazauna tabbacin samun tsaro, ya ce an fara bincike a kan kisan bakin ciki da ke faruwa a fadin jihar.

Ya bayyana cewa musamman yan sanda suka shiga bincike da tura jami’ai wurare masu muhimmanci a jihar.

Kara karanta wannan

Rundunar yan sanda ta tabbatar da kisan mutum 12 a wani harin sassafe da yan bindiga suka kai Katsina

Ina gab da haukacewa: Mijin mata da 'ya'ya 4 da IPOB suka kashe ya magantu

A gefe guda, mun ji cewa magidancin da ya rasa matarsa mai tsohon ciki da 'ya’ya hudu a jihar Anambra, ya bayyana cewa ya ji kamar ya yi hauka sakamakon tashin hankalin da ya tsinci kansa a ciki.

Tsagerun yan bindiga da ake zaton yan kungiyar awaren IPOB ne suka kai farmakin inda suka hallaka mutane 12 ciki harda matar mai tsohon ciki, Harira Jibril da yaranta su hudu.

Mijin matar kuma uba ga yara hudun da aka kashe a harin ya shaida wa BBC cewa an kashe iyalin nasa ne a lokacin da suke kan hanyar su ta dawowa daga ziyarar da suka kai a yankin Orumba ta arewa a jihar Anambra.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng