Abin Da Yasa Muka Yi Dirar Mikiya a Gidan Okorocha, EFCC Ta Magantu

Abin Da Yasa Muka Yi Dirar Mikiya a Gidan Okorocha, EFCC Ta Magantu

  • Hukumar yaki da rashawa da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati ta EFCC ta bayyana dalilin da yasa jami'anta suka tafi gidan Sanata Rochas Okorocha
  • Hukumar ta EFCC ta ce tsohon gwamnan na Jihar Imo ya tsallake belin da aka bashi a baya kuma ya ki amsa gayyatar da aka yi ta yi masa
  • Wilson Uwujaren, kakakin EFCC cikin takardar da ya fitar ya ce kotu ta yi barazanar cewa ba za ta saurari shari'ar ba idan ba a gurfanar da shi Okorocha a ranar 30 ga watan Mayu ba

Hukumar Yaki da rashawa da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta yi bayanin dalilin da yasa jami'anta suka yi dirar mikiya a gidan tsohon gwamnan Jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha a ranar Talata.

Kara karanta wannan

An ki cin biri, an ci dila: Yadda sabon AGF ke da jikakkiyar tuhumar rashawa da EFCC

Da ya ke magana kan dalilin zuwan EFCC gidansa a ranar Talata, Sanata Rochas ya zargi hukumar da yi masa daurin talala a gidansa tare da hana shi zuwa wurin tantance yan takarar shugaban kasa na APC.

A cewar hukumar, ta bakin kakakinta Wilson Uwujaren Sanata Rochas ya ki amsa gayyatar da aka yi masa ne lokuta da dama bayan ya tsallake beli, Channels Television ta rahoto.

Abin Da Yasa Muka Yi Dirar Mikiya a Gidan Okorocha, EFCC Ta Magantu
Abin Da Yasa Muka Yi Dirar Mikiya a Gidan Okorocha, EFCC. Hoto: Channels Television.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ranar 24 ga watan Janairun 2022, EFCC ta shigar da kara kan tuhume-tuhume masa alaka da karkatar da kudin gwamnati da kadarori na kimanin N2.9bn kan Okorocha a cewar Uwujaren.

Ya ce an mika shari'ar ne ga Mai Shari'a Inyang Ekwo ta babban kotun tarayya da ke Abuja amma an yi kokarin gurfanar da Okorocha har sau biyu sai dai ya rika zille wa hukumar.

Kara karanta wannan

Bayan EFCC ta kewaye gidansa, Rochas Okorocha ya faɗi gaskiyar halin da yake ciki da mataki na gaba

Wilson ya kara da cewa:

"A ranar da aka so gurfanar da shi ta karshe, ranar 28 ga watan Maris, Mai shari'a Ekwo kafin dage gurfanarwar zuwa ranar 30 ga watan Mayun 2022, ta yi gargadin cewa 'wannan shine karo na karshe da zan dage gurfanarwa kan wannan shari'ar.'
"A wannan yanayin da ake ciki, hukumar ba ta da wani zabi illa ta kama Sanata Rochas Okorocha domin kai shi kotu a gurfanar da shi."

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164