Idan ba'a saki kwamandojinmu ba, ba za'a sake amfani da jirgin kasa da titin Abuja-Kaduna ba: Yan ta'adda
- Yan ta'addan da suka hallaka mutane kuma suka kashe wasu a jirgin kasan Abuja-Kaduna sun bayyana bukatunsu
- Yan bindigan sun baiwa gwamnatin tarayya daman cin musanyan fursunoni tsakanin wadanda suka sace da kwamandojinsu
- Yan ta'addan sun ce wannan shine kadai abinda zai sa su saki mutum 62 dake hannunsu
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Yan ta'addan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna sun yi barazanar hana amfanin da titin Kaduna-Abuja gaba daya idan gwamnatin tarayya bata saki yan'uwansu ba.
Shugaban yan ta'addan, Abu Barrah, ya bayyana hakan ne ga Tukur Mamu, shugaban kamfanin jaridar Desert Herald.
Abu Barrah ya kara da cewa saboda su gwamnatin tarayya ta dage ranar dawo da amfani da jirgin kasan.
Yace:
"Zamu saki sauran fasinjojin idan aka saki wasu kwamandojinmu dake hannun gwamnati."
"Idan gwamnati taki amsa bukatunmu. Muna gargadin yan Najeriya musamman masu hawa jirgin kasa da bin titin Abuja su daina saboda zamu fara kai hari ba kakkautawa kuma babu wanda ya isa ya hanamu."
Harin jirgin kasan Abj-Kad: An nemo 'ya'ya 8 na 'yan ta'adda, ana shirin mika musu don fansar fasinjoji
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ba su bukatan kudi
Shugaban yan ta'addan ya kara da cewa ba su bukatan kudi. Kuma zasu ga cewa wadanda ke hannunsu na cikin koshin lafiya.
Yace:
"Bamu bukatan kudi. Muna da dalilin yin abinda muka yi, kuma idan ba'a biya bukatunmu ba, babu fasinja da zai fito da rai ko da zamu mutu tare ne."
Ya ce sun aike wa Tukur Mamu sakonsu ne saboda suna ganinsa tare da Sheikh Gumi a cikin daji.
Harin jirgin Abuja-Kaduna: Sulhu kadai ne mafita wajen ceto sauran fasinjojin, Wacce yan bindigan suka saki
Thamina Mahmood na daya daga cikin mutum 62 da yan ta'addan suka sace a harin da suka kai jirgin kasan Abuja-Kaduna ranar 28 ga watan Maris, 2022.
Thamina, wacce ke dauke da juna biyu ta samu kubuta saboda halin da take ciki kuma ta bayyana abubuwan da suka faru.
A hirarta da Daily Trust, ta yi bayanin cewa sulhu kadai ne mafita wajen ceto sauran wadanda ke hannun yan bindigan.
Kwanakin baya kafafen yada labarai sun ruwaito cewa Thamina ta haihu a hannun yan bindiga, amma yanzu tace ba gaskiya bane.
Asali: Legit.ng