Ku saki 'yayanmu 8 dake hannunku a Yola sai mu saki fasinjojin jirgin kasan Abuja: Yan ta'addan
- Yan ta'addan da suka hallaka mutane kuma suka kashe wasu a jirgin kasan Abuja-Kaduna sun bayyana bukatunsu
- Sun baiwa gwamnatin tarayya wa'adi ta sake musu 'yayansu da gwamnati ta garkame a jihar Adamawa
- Yan ta'addan sun ce wannan shine kadai abinda zai sa su saki mutum 62 dake hannunsu
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Yan ta'addan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna sun yi barazanar fara kashe wadanda suka kwashe idan gwamnatin tarayya bata saki yaransy dake hannunta ba.
Shugaban yan ta'addan, Abu Barrah, yace gwamnati ta ajiye 'yayansu a gidan marayu dake Yola.
Abu Barrah ya bayyana hakan ne ga Tukur Mamu, shugaban kamfanin jaridan Desert Herald.
Yace:
" 'Yayanmu guda 8 masu shekaru 1 - 7 na tsare a gidan marayu dake Jimeta, jihar Adamawa karkashin jagorancin hukumar Sojin Najeriya."
"Sunan 'yayanmu; Abdulrahman, Bilkisu, Usman, Ibrahim and Juwairiyyah. An kwashesu ne daga hannun matanmu a jihar Nasarawa kuma aka kaisu gidan marayu a Yola."
Harin jirgin kasan Abj-Kad: An nemo 'ya'ya 8 na 'yan ta'adda, ana shirin mika musu don fansar fasinjoji
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Kafin mu saki fasinjojin da cigaba da aikin jirgin kasan, wajibi ne a saki 'yayanmu."
Ya kara da cewa idan aka saki 'yayan na su, zasu saki fasinjoji mata kadai.
Yace idan gwamnati bata sake su ba, zasu kashe fasinjojin daya bayan daya.
Harin jirgin Abuja-Kaduna: Sulhu kadai ne mafita wajen ceto sauran fasinjojin, Wacce yan bindigan suka saki
Thamina Mahmood na daya daga cikin mutum 62 da yan ta'addan suka sace a harin da suka kai jirgin kasan Abuja-Kaduna ranar 28 ga watan Maris, 2022.
Thamina, wacce ke dauke da juna biyu ta samu kubuta saboda halin da take ciki kuma ta bayyana abubuwan da suka faru.
A hirarta da Daily Trust, ta yi bayanin cewa sulhu kadai ne mafita wajen ceto sauran wadanda ke hannun yan bindigan.
Kwanakin baya kafafen yada labarai sun ruwaito cewa Thamina ta haihu a hannun yan bindiga, amma yanzu tace ba gaskiya bane.
Asali: Legit.ng