Bayan wata 2 da 'yan ta'adda suka kai hari, an sake bude filin jiragen sama na Kaduna

Bayan wata 2 da 'yan ta'adda suka kai hari, an sake bude filin jiragen sama na Kaduna

  • An sake bude filin sauka da tashin jiragen sama na Kaduna bayan wata biyu da tayi a rufe bayan farmakin 'yan bindiga
  • Kamfanin jiragen sama na Azman ne suka fara sauke fasinjoji a filin bayan farmakin 'yan ta'adda a watan Maris
  • An garkame filin jirgin saman ne bayan 'yan ta'adda suna kai farmaki da tsakar rana har cikin filin jiragen saman

Kaduna - Filin sauka da tashin jiragen sama na Kaduna ya cigaba da aiki bayan watanni biyu da aka rufe shi sakamakon farmakin da 'yan bindiga suka kai a watan Maris.

Faithful Hope-Ivbaze, mukaddashin babbar manajan al'amuran gudanarwa na FAAN, ta tabbatar da hakan ga TheCable a ranar Litinin.

Bayan wata 2 da 'yan ta'adda suka kai hari, an sake bude filin jiragen sama na Kaduna
Bayan wata 2 da 'yan ta'adda suka kai hari, an sake bude filin jiragen sama na Kaduna. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

"Jiragen sama sun fara sauka da tashi a filin jirgin na Kaduna a yau inda aka fara da Azman Air," tace.

Kara karanta wannan

Kuma dai: ‘Yan bindiga sun farmaki ofishin yan sanda a Anambra, sun kona motoci

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

TheCable ta ruwaito yadda 'yan bindiga suka kai farmaki filin sauka da tashin jiragen sama inda suka halaka wani mai gadi.

Sai dai, babu kakkautawa jami'an tsaro suka fatattaki 'yan ta'addan.

A daya bangaren, Azman Air ta sanar da cigaba ayyukan jiragenta a filin jirgin sama na Kaduna, hakan yasa kamfanin ya zama na farko da ya dawo da al'amuransa tun bayan aukuwar lamarin.

Hukumar kamfanin jirgin saman ta ce za ta dakatar da ayyukanta na kwanaki kadan sakamakon farmakin.

A yayin karin bayani kan inda aka kwana a wata wallafar Twitter da kamfanin jirgin sama yayi, yace jirgin su ya taba kasar filin a ranar Litinin.

"Jirgin Azman ya sauka a Kaduna a yau, 23 ga watan Mayun 2022 cike da murna tare da farin cikin fasinjoji, masu ruwa da tsaki da ma'aikata," Azman Air ta wallafa.

Kara karanta wannan

Cikin katatafaren kadarorin da suka tsunduma AGF Ahmed Idris a komar EFCC

"Wannan lokaci ne mai ma'ana ga bangaren sufurin jiragen sama yayin da aka bude filin jirgin saman bayan wata biyu da rufewa. Mun fada farin ciki a yayin da muka dawo!"

Harin filin jirgin saman Kaduna: 'Yan bindiga tserewa suka yi da ganin jami'anmu, gidan soja

A wani labari na daban, hukumar soji a ranar Litinin, 28 ga watan Maris, ta bayyana cewa yan bindiga basu isa su kai farmaki filin jirgin sama na Kaduna ba.

Da take martani kan kisan wani jami’in hukumar NAMA, rundunar tace lamarin ya faru ne kimanin kilomita shida dagatashar jirgin da kuma wajen katangar filin jirgin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel