Da Dumi-Dumi: Bayan kokarin sulhu, Gwamna Soludo ya shata layin yaƙi da yan bindiga a Anambra

Da Dumi-Dumi: Bayan kokarin sulhu, Gwamna Soludo ya shata layin yaƙi da yan bindiga a Anambra

  • Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya zana layin yaƙi da masu aikata manyan laifuka a jihar Anambra
  • Gwamnan, wanda a farkon gwamnatinsa ta mika hannun sulhu ga yan bindiga, ya ce ba zasu sake samun filin aikata ta'addanci
  • Ya yaba wa mambobin jam'iyyarsa ta APGA bisa ɗumbin goyon bayan da suka ba shi har ya samu nasara a zaɓen da ya gabata

Anambra - Biyo bayan ƙara taɓarɓarewar tsaro a Anambra, gwamnan jahar, Farfesa Charles Soludo, ya ce gwamnatinsa ta shata layin yaƙi da masu ta da ƙayar baya.

Jaridar Vanguard ta rahoto gwamnan na jaddada cewa daga yanzun ba zasu sake samun sakat ba balle su kai hari kan mutanen da ba ruwan su.

Da yake jawabi ga yan takarar jam'iyyar APGA na kujerun siyasa daban-daban a zaɓen 2023, Gwamna Soludo ya ce tuni gwamnatinsa ta fara ɗaukar matakai da haɗin kan hukumomin tsaro don kawo karshen tashe-tashen hankula a jihar.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ga Najeriya: Ba zan huta ba har sai an samu zaman lafiya a kasar nan

Farfesa Charles Soludo na jihar Anambra.
Da Dumi-Dumi: Bayan kokarin sulhu, Gwamna Soludo ya shata layin yaƙi da yan bindiga a Anambra Hoto: vanguardngr.com

Fafesa Soludo ya ce gwamnatinsa ba zata runtsa ba har sai ta kawo karshen damuwar mutane, zaman lafiya da kwanciyar hankali ya samu gindin zama.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma koka da kisan gillan da yan ta'adda suka yi wa ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Aguata a majalisar dokokin Anambra, Okechukwu Okoye, tare da hadiminsa.

Ya sha alwashin cewa duk waɗan da suka aikata wannan kisan na rashin imani za'a binciko su kuma su girbi abin da da suka shuka.

Soludo yace lalacewar matsalar tsaro a jihar, "Masu aikata laifuka ne suka ƙara ta'azzara lamarin ta hanyar shiga garkuwa da mutane, kisa da sauran ayyukan laifi manya."

Soludo ya yaba wa APGA bisa goyon baya a zaɓen Anambra

Bayan haka gwamnan ya yaba wa mambobin jam'iyyarsa ta APGA bisa ɗumbin goyon bayan da ya samu har ta kai ga nasara da zaben Anambra daya gabata.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya bayyana irin yadda yake matukar son gaje Buhari, ya ce ba wasa yake ba

Ya kuma nuna kwarin guiwarsa cewa APGA zata ba da mamaki, zata lashe kujerun yan majalisun jiha da na tarayya a babban zaɓen 2023 da ke tafe.

A wani labarin na daban kuma Kungiyoyin Musulmai 13 sun aike da sako ga Gwamnatin Buhari game da Zagin Annabi SAW

Kungiyoyin Musulmai 13 sun yi kira ga gwamnati ta yi wa waɗan da aka kama da kashe Deborah Samuel adalci.

Kungiyoyin ƙarƙashin inuwar MURIC mai fafutukar kare haƙƙin musulmai a Najeriya sun shawarci gwamnati kan hanyar kawo karshen irin haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262