Cikin katatafaren kadarorin da suka tsunduma AGF Ahmed Idris a komar EFCC
- Hukumar EFCC ta yi ram da akanta janar AGF Ahmed Idris bayan zarginsa da kwashe N80 biliyan daga lalitar gwamnatin tarayya
- Daga cikin manyan kadarorin da suka kai shi ga komar EFCC akwai katafaren gin kantin Al-Ikhlas da ya ke tamfatsawa a Kabara, Kano
- Ginin kasuwar Gezawa mai darajar N4.5 biliyan ya zama abun mamaki da ya sa aka fara tantamar halascin dukiyar Ahmed Idris
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kano - Kusan mako daya da jami'an hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, suka kama akanta janar na tarayya, Ahmed Idris, kan zarginsa da waskar da N80 biliyan daga lalitar gwamnati, ana cigaba da cece-kuce bayan fallasar da EFCC ta yi masa.
A ranar Litinin hukumar yaki da rashawan ta yi ram da shi yayin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa Kano bayan ya gaza amsa gayyatar da suka tura masa.
Har zuwa ranar Juma'a, babban jami'in gwamnatin yana hannun jami'an hukumar inda yake amsa tambayoyi masu yawa da suka hada da na zargin wanke kudin haram da waskar da kudaden gwamnati.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hukumar ta zargi cewa Idris ya boye kudaden ne ta hanyar siyan kadarori a sassa daban-daban na kasar nan.
Binciken Daily Trust ya bayyana cewa jami'in gwamnatin ya mallaki katafarun kadarori a cikin garin Kano. Sauran suna watse a Legas, Abuja, Dubai da London.
Daya daga cikin manyan kadarorinsa da Legit.ng ta gani shi ne katafaren ginin da ake tafkawa a inda tsohon katafaren kantin Al-Ikhlas ya ke a Kabara da ke birnin Kano daura da fitaccen kantin Sahad na farko da ke Kano.
Bayanai daga mazauna yankin sun bayyana yadda yake siyan gidajen da ke kusa da tsohon kantin Al-Ikhlas inda yake ta fadada wurin.
Majiyoyi masu karfi sun sanar da yadda Idris ke siyan kadarori a birnin Kano inda yake mayar da wasu makarantun kudi da asibitoci.
Karin bincike ya bayyana yadda dakataccen akanta janar ya ke da gidaje na miliyoyin naira a kwatas din Gandu.
Daily Trust ta ruwaito cewa, gidajensa na miliyoyin naira a GRA Ladanai duk a Kano ya janyo cece-kuce da tambayoyi kan halascin kudaden Idris wanda aka fi sani da Mai Kanti a Kabara.
Baya ga sauran kadarorinsa, daya daga cikin katafarun kadarorin Idris sun hada da Gezawa Commodity and Exchange Market da ke karamar hukumar Gezawa ta jihar Kano wacce ta kai darajar N4.5 biliyan.
An bai wa kasuwar lasisin fara aiki a shekarar 2021.
Damfarar N80bn: ASUU ta zunɗi AGF, ta ce FG ta yi watsi da tsarin IPPIS
A wani labari na daban, a ranar Talata, kungiyar malaman jami'a masu koyarwa (ASUU) ta bukaci gwamnatin tarayya da tayi watsi da tsarin biyan ma'aikata na IPPIS da take amfani dashi wajen biyan ma'aikatan tarayya albashi.
ASUU ta yi martani game da cafke akawu janar na tarayya, Ahmad Idris da hukumar EFCC tayi bisa zarginsa da almundahana, tare da sunkuce N80 biliyan jaridar Newswire ta ruwaito.
Asali: Legit.ng