Bayan gano gidajensa 17 a gida da waje, kotu ta baiwa EFCC daman cigaba da rike Akanta Janar

Bayan gano gidajensa 17 a gida da waje, kotu ta baiwa EFCC daman cigaba da rike Akanta Janar

  • EFCC ta samu izini daga kotu na cigaba da tsare Akanta Janar hannunsu har a kammala bincike
  • Bincike ya nuna cewa ya mallaki gidaje goma sha bakwai a Dubai, Landan, Abuja, Kano da jihar Legas
  • Hukumar za ta gurfanar da shi gaban kotu bayan kammala bincike kan yadda yayi rub da ciki da N80bn

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta samu izinin kotu don cigaba da rike Akanta Janar na tarayya, Ahmed Idris.

Wani jami'in hukumar wanda aka sakaye sunansa ya bayyana cewa hukumar ta samu izinin ne cikin kwana 1 da kama shi, rahoton Daily Trust.

Ya ce an basu daman su cigaba da tsareshi har sai an kammala bincikensa.

Yace:

"Har yanzu yana wajenmu kuma yana bada hadin kai. Zamu bankado komai. Dadin abin shine lauyoyinmu sun samu umurnin kotu na cigaba da tsareshi har mu kammala bincike."

Kara karanta wannan

Titin Abuja-Kaduna: El-Rufa'i ya bada shawarar tayar da wasu garuruwa uku dake kan hanyar

Yayinda aka tambayesa yaushe za'a sake shi, jami'in yace ai nan ba da dadewa ba za'a gurfanar da Ahmed Idris gaban kotu saboda hujjojin da aka samu kansa na da ban tsoro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Akanta Janar
Bayan gano gidajensa 17 a gida da waje, kotu ta baiwa EFCC daman cigaba da rike Akanta Janar Hoto: HouseNGR
Asali: Twitter

An gano gidajensa guda 17 a Landan, Abuja, Legas, Kano da Dubai

EFCC ta bankado gidajen Akanta Janar na tarayya, Ahmad Idrs, guda goma sha bakwai (17).

Punch ta ruwaito cewa wani jami'in EFCC wanda ya bukaci a sakaye sunansa yace Idris ya mallaki gidaje a Kano, Lagos, Abuja, Dubai da London

Ya kara da cewa an gani Ahmad Idris ya yi amfani da wasu makusantarsa wajen sayen wadannan dukiyoyi.

A cewarsa da yiwuwan ya sadaukarwa gwamnati wadannan gidaje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel