MNJTF sun bankado kasuwar ISWAP, sun damke 'yan ta'adda 30 a yankin tafkin Chadi

MNJTF sun bankado kasuwar ISWAP, sun damke 'yan ta'adda 30 a yankin tafkin Chadi

  • Jami'an MNJTF sun yi ram da 'yan ta'adda 30 a yayin wani sintiri da suka je har kasuwar kifi ta Boko Haram a yankin tafkin Chadi
  • Bincike ya tabbatar da cewa a wannan kasuwar ne 'yan Boko Haram ke siye da siyarwa tare da samun kudaden siyan makaman ta'addanci
  • Sabon bincike ya nuna yadda 'yan kasuwa ke bin wata hanya zuwatafkin Chadi kuma suke biyan 'yan Boko Haram harajin N5,000 duk wata

Borno - Jami'an rundunar hadin guiwa ta kasashe, MNJTF sun bankado kasuwar kifi ta Boko Haram a yankin tafkin Chadi kuma sun kama mutane 30 da suka yi ikirarin cewa su masunta ne da manoma, majiyar tsaro ta tabbatar.

An gano cewa kasuwar ce babban jigon samun kudi ga 'yan ta'addan wanda suke amfani da shi wurin siyan makamai da harsasai.

Kara karanta wannan

Borno: Jirgin NAF ya yi amon wuta kan tawagar Boko Haram/ISWAP, 'yan ta'addan sun salwanta

MNJTF sun bankado kasuwar ISWAP, sun damke 'yan ta'adda 30 a yankin tafkin Chadi
MNJTF sun bankado kasuwar ISWAP, sun damke 'yan ta'adda 30 a yankin tafkin Chadi. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Dakarun sun gano kasuwar kifi a wani babban sintirin da suka je Tamfalla, fitacciyar kasuwar kifi da ke karamar hukumar Kukawa," wata majiya tace.

Kwararre wurin yaki da ta'addancin kuma mai kiyasi kan tsaro da ilimin sanin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya tabbatar da kamen 'yan ta'addan, PRNigeria ta ruwaito.

Yayin bayar da karin bayani kan aikin, jami'in yada labarai na MNJTF na N'Djamena, Laftanal Kanal Kamarudeen Adegoke, ya ce an kama matasa 30 wadanda suka yi ikirarin cewa su masunta ne da manoma. An cafke su a yankin Doron Naira kuma an ayyanasu matsayin 'yan ta'adda kuma ana tuhumarsu.

Ya ce an kama kifaye a kwalaye, kifayen da aka gyara, hatsi, kayan amfanin gida da babur.

An gano cewa ISWAP na cigaba da watsa ta'addancinta ta hanyar masunta, manoma da masu kiwon shanu tare da wasu al'amuran tattalin arziki a yankin tafkin Chadi.

Kara karanta wannan

Batanci ga Annabi: Gwamnati ta cire takunkumi a Sokoto, ta haramta zanga-zanga

Vanguard ta gano cewa 'yan ksuwa daga Maiduguri, Adamawa, Monguno, Hadejia, Nijar da Kamaru na satar hanya zuwa tafkin Chadi ta hanyar da a halin yanzu ta ke lafiya kalau.

"A saboda haka, ISWAP na karbar N5,000 na haraji a kowanne wata daga duk wanda ke son bin hanyar," wata majiya tace.

Sun kara da samun hanyar zuwa kasuwanci, abu mafi amfani da kiyayewa shi ne su cigaba da bai wa ISWAP kudadensu.

Borno: Jirgin NAF ya yi amon wuta kan tawagar Boko Haram/ISWAP, 'yan ta'addan sun salwanta

A wani labari na daban, a karshen makon nan, dakarun sojin sama na Operation Hadin Kai sun kai wa 'yan Boko Haram da mayakan ISWAP samame inda suka sheke tarin 'yan ta'adda da dama yayin wani farmaki a jirgin sama a arewa maso gabacin Borno, Zagazola ya tabbatar.

Wata babbar majiyar sirri ta bayyanawa Zagazola Makama, wani kwararren mai rahoton lamurran ta'addanci a yankin tafkin Cadi, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rudani: 'Yan bindiga sun sako hakimin kauyen Kano, sun rike farfesan da ya kai kudin fansa

Majiyoyi sun labarta yadda aka yi nasara a samamen da aka kai a ranar 21 ga watan Mayu a Wara Wara - wani kauye a karamar hukumar Damboa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng