Borno: Jirgin NAF ya yi amon wuta kan tawagar Boko Haram/ISWAP, 'yan ta'addan sun salwanta

Borno: Jirgin NAF ya yi amon wuta kan tawagar Boko Haram/ISWAP, 'yan ta'addan sun salwanta

  • Dakarun sojin sama na Operation Hadin Kai sun kai samame ga 'yan Boko Haram da tawagar mayakan ISWAP gami da sheke tarin 'yan ta'addan a wata musayr wuta a Borno
  • Wata babbar majiyar sirri ce ta bayyana hakan ga Zagazola Makama, wani shahararren mai rahoton lamurran ta'addanci a yankin tafkin Chadi
  • A cewar majiyar, misalin karfe 1:30 na dare, tawagar'yan ta'addan ta nufi Wara Wara - don birne gawawwakin mayakan ISWAP din da aka sheke gami da yi musu sallar jana'iza

Borno - A karshen makon nan, dakarun sojin sama na Operation Hadin Kai sun kai wa 'yan Boko Haram da mayakan ISWAP samame inda suka sheke tarin 'yan ta'adda da dama yayin wani farmaki a jirgin sama a arewa maso gabacin Borno, Zagazola ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wata Mata Ta Sake Zagin Annabi a Bauchi, Matasa Sun Bazama Nemanta, Sun Ƙona Gidaje Sun Raunta Fasto

Wata babbar majiyar sirri ta bayyanawa Zagazola Makama, wani kwararren mai rahoton lamurran ta'addanci a yankin tafkin Cadi, Vanguard ta ruwaito.

Borno: Jirgin NAF ya yi amon wuta kan tawagar Boko Haram/ISWAP, 'yan ta'addan sun salwanta
Borno: Jirgin NAF ya yi amon wuta kan tawagar Boko Haram/ISWAP, 'yan ta'addan sun salwanta. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Majiyoyi sun labarta yadda aka yi nasara a samamen da aka kai a ranar 21 ga watan Mayu a Wara Wara - wani kauye a karamar hukumar Damboa.

Majiyar ta kara da bayyana yadda ta cigaba da dauko jiragen yakin sama don ganin an ragargaji hatsabiban, luguden wutar ya yi nasarar sheke wata tawagar hatsabiban.

Yayin cigaba da bayani, majiyar ta ce luguden wutar da aka aiwatar da taimakon Operation Desert Sanity, bayan tarin binciken da ya nuna ayyukan 'yan ta'adda wuraren Korede, Shettim Affor, kauyen Kalolowa da kauyen Wara Wara dake Damboa ya haifar da abinda ake so.

Shahararren mai binciken sirri da lura da lamurran ta'addanci a tafkin Cadi, Zagazola Makama ya tabbatar da yadda samamen ya gabata inda ya ce jiragen saman yakin sun kai farmaki gami da tarwatsa motocin bindiga hudu tare da halaka mayaka da dama yayin kai harin.

Kara karanta wannan

Ke duniya: 'Yan sanda sun damke magidanci da ya tura matarsa karuwanci, ya siyar da 'dan shi

A cewarsa, misalin awanni 1:30 na dare, tawagar 'yan ta'addan ta doshi Wara Wara - don birne wasu daga cikin mattatun dakarun 'yan ta'addan gami da nufar kauyen Litawa, a yankin Damboa, wani wuri da daga bisani za su yi wa mattatun sallar gawa.

Kungiyar ta'addancin Ansaru na diban ma'aikata a Kaduna, suna raba goron Sallah

A wani labari na daban, mambobin kungiyar ta'addanci ta Ansaru sun fara diban aiki inda suka daukan mazauna yankin karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, jaridar Daily Trust ta tattaro.

Ansaru, wani sashin kungiyar ta'addanci ne na Boko Haram kuma sun kasance suna cin karensu babu babbaka a kauyukan Birnin Gwari na tsawon shekaru.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel