Cakwakiya: Wata mata ta ba da labarin yadda ta auri yayanta har suka haifi 'ya'ya 4

Cakwakiya: Wata mata ta ba da labarin yadda ta auri yayanta har suka haifi 'ya'ya 4

  • Kamar dai yadda ake gani daga fina-finan Nollywood, wata mata ta ba da labarin yadda ta auri dan uwanta ba tare da saninsa ba
  • Matar mai suna Domitila ta taso ne ba tare da ta san tana da dan uwa ba kuma ba ta ma san iyayenta ko kamanninsu ba
  • Ta shilla birni ne tun tana budurwa domin neman aiki sannan ta hadu da yayanta sai suka fara soyayya ta aure ba tare da sun sani ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wata mata mai suna Domitila ta ce ta auri dan uwanta cikin rashin sani saboda bata taba sanin tana da yaya ba.

Kamar yadda labarin ya nuna, iyayensu sun yi watsi da su ne tun suna kanana kuma a haka suka watsu a wurare daban-daban babu mai kula da su.

Matar da ta auri yayanta suka haif 'ya'ya 4
Cakwakiya: Wata mata ta ba da labarin yadda ta auri yayanta har suka haifi 'ya'ya 4 | Hoto: YouTube/Afrimax English
Asali: UGC

Sun girma a wurare daba-daban

Kara karanta wannan

Boka ya dirkawa matar aure ciki, rikici ya barke tsakaninsa da mijinta: Ga labarin dalla-dalla

Babu daya daga cikin ’yan’uwan biyu da ya san cewa suna da dangantaka domin ba su girma tare ba duba da yadda iyayensu suka watsar dasu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Domitila ta tafi birni nemo aiki sai kawai ta kamu da soyayyar yayanta ba tare da ta sani ba.

Sun haifi 'ya'ya hudu

Daga baya sun yi aure har suka haifi ’ya’ya hudu kafin mutanen su gano cewa suna da asali da tushe daya.

Bayan gano lamarin mai ban mamaki, jama'a sun mai da Domitila saniyar ware saboda babu wanda ke son alaka da ita.

'Ya'yanta duk sun yi kama da nakasassu kuma hakan yasa mutane a ke ganin hakan a matsayin illar auren 'yan ciki daya.

Domitila ta kasa jurewa wannan abin kunyar, ta raba auren, ta dauki ‘ya’yanta hudu domin ci gaab da rayuwa a wani rugujewar gida kafin su samu tallafin wata kungiya mai zaman kanta da aka fi sani da Giving Life Foundation.

Kara karanta wannan

Tsaleliyar Budurwa Za Ta Auri Direban Napep Da Ta Ba Wa Lambar Wayarta Shekaru 5 Da Suke Shuɗe

Kungiyar ta siya mata sabon gida ta kuma baiwa da ‘ya’yanta sabon gobe. Afrimax English ya yada bidiyo mai ban mamaki na labarin.

Kalli bidiyon:

'Yan YouTube sun yi martani

Mukunzi Ntusi:

"Wadanda suka la'ance su yanzu suna yi musu hassada, babu wani yanayi da zai dawwama, ku dogara ga Allah, nagode muku duk wadanda suka ba da gudummawa wajen ganin hakan ya faru, Allah Ya saka muku da alheri."

Flurance Mbone:

"Allah ya sakawa afrimax kuma ya cigaba da yiwa wannan ahali albarka."

Okwy Frank:

"Lallai Allah mai girma ne, Allah ya sakawa wanda ya tallafa ya kuma albarkaci Afrimax wanda Allah ya ke amfani da shi don daga mutane daga matsanancin talauci."

Na Allah Ba Su Ƙarewa: Bidiyon Direban Napep Da Ya Mayar Wa Fasinja Kwamfutarsa Har Gida Bayan Ya Yi Mantuwa

A wani labarin, wani dan Najeriya ya yaba wa wani direban Keke Napep inda ya bukaci mutane da su kasance masu shiga kekensa duk inda su ka gan shi.

Kara karanta wannan

Fashewar tukunyar gas a Kano: Harkoki sun daidaita amma iyaye sun ki mayar da yaransu makaranta

Mutumin, wanda injiniya ne ya yi wata wallafa a shafinsa na Twitter akan yadda Direben Keken ya mayar masa da na’ura mai kwakwalwarsa wato kwamfuta bayan ya manta da ita.

@Hakmansclothing ya ce ya mantar da ita ne kasancewar ya dauko kaya masu tarin yawa. Bayan sa’o’i uku da komawarsa gida sai mai gadin gidansa ya sanar da shi cewa wani direban Keke Napep ya na nemansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.