Na Allah Ba Su Ƙarewa: Bidiyon Direban Napep Da Ya Mayar Wa Fasinja Kwamfutarsa Har Gida Bayan Ya Yi Mantuwa

Na Allah Ba Su Ƙarewa: Bidiyon Direban Napep Da Ya Mayar Wa Fasinja Kwamfutarsa Har Gida Bayan Ya Yi Mantuwa

  • Wani mutum ya yi wata wallafa a shafinsa na kafar sada zumunta inda ya nuna irin gaskiya da rikon amanar da wani direban Keke Napep ya nuna masa
  • Kamar yadda ya nuna, ya mantar da na’ura mai kwakwalwarsa ne a cikin Keken mutumin kasancewar ya dauko shi da kaya masu yawan gaske
  • Abin da ya ba shi mamaki shi ne yadda direban Napep din ya koma har gidan da ya ajiye shi ya nemi shi don mayar masa da mantuwar ta shi

Wani dan Najeriya ya yaba wa wani direban Keke Napep inda ya bukaci mutane da su kasance masu shiga kekensa duk inda su ka gan shi.

Mutumin, wanda injiniya ne ya yi wata wallafa a shafinsa na Twitter akan yadda Direben Keken ya mayar masa da na’ura mai kwakwalwarsa wato kwamfuta bayan ya manta da ita.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Direban Keke Napep ya koma gidan fasinja ya mayar mishi da kwamfutar shi da ya manta a kekensa
Direban Napep ya koma gidan fasinja ya mayar mishi da kwamfutar shi da ya manta a kekensa. Hoto: @Hakmansclothing
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

@Hakmansclothing ya ce ya mantar da ita ne kasancewar ya dauko kaya masu tarin yawa. Bayan sa’o’i uku da komawarsa gida sai mai gadin gidansa ya sanar da shi cewa wani direban Keke Napep ya na nemansa.

Kamar yadda ya ce, ya yi mamakin ganin wannan direban Napep din wanda ya kai shi gida ya dawo masa da na’ura mai kwakwalwar da ya manta da ita.

Anan ya dauki bidiyonsu a tare yana yaba masa akan gaskiyarsa da rikin amana.

A wallafar da Injiniyan ya yi ya ce:

“Washegarin sallah aka yi wannan. Na debo kaya masu yawa sai na mance da na’ura mai kwakwalwata a bayan Napep. Yanzu haka ya dawo min da ita har gida bayan kwashe sa’o’i da ajiye ni saboda tsorin Ubangijinsa.”

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya

Tsokacin ‘yan Najeriya karkashin wallafar

Anoneme2 ta ce:

“Wannan abin birgewa ne daga cikin halayyar musulunci da musulmai.”

beautyinnocent ya ce:

“Gaskiya ne wannan. Masu kirkinsu su na da mutunci kwarai. Hmmm.”

Echelonable ya ce:

“Kuma ba ka ba shi komai ba ko...hakan daidai ne...?”

efirstconsults ya ce:

“Kuma ba ka ba shi komai ba?”

zagga1_hot ya ce:

“Su na da kirki sosai, kawai dai su na da saurin fushi idan har ka bata musu rai...hmmmm.”

Shugaban wurin aiki ya ba na ƙasa da shi da ke tattaki zuwa wurin aiki kyautar mota

A wani rahoton, wani matashi, Walter, ya yi tattakain mil 20 a ranar sa ta farko ta zuwa wurin aiki. Motarsa ta samu matsala ana gobe zai fara zuwa aikin hakan ya sa ya yanke wannan shawarar.

Kafin safiyar, ya yi kokarin tuntubar abokan sa amma babu alamar zai samu tallafi saboda ya sanar da su a kurarren lokaci kamar yadda Understanding Compassion ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mai neman takarar Shugaban kasa ya tona asirin masu karyar sayen fam a jam’iyyar APC

Daga nan ne ya yanke shawarar fara tattaki tun karfe 12am don isa wurin aikin da wuri. Matashin bai bari rashin abin hawan ya dakatar da shi ba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel