Kashe Deborah a Sokoto: Yan sanda sun gana da Malaman Musulunci da masu ruwa da tsaki

Kashe Deborah a Sokoto: Yan sanda sun gana da Malaman Musulunci da masu ruwa da tsaki

  • Hukumar yan sanda reshen jihar Zamfara ta gana da Malaman addini da masu faɗa aji biyo bayan kashe ɗalibar da ta zagi Annabi SAW a Sokoto
  • Kwamishinan yan sandan Zamfara, Ayubah Elkanah, ya yi kira ga mutane su giji ɗaukar doka a hannun su, su kai korafi ga hukumomin tsaro
  • Mahalarta taron sun yaba da namijin kokarin hukumar yan sanda, sun sha alwashin ba da ta su gudummuwar

Zamfara - A yunkurin dakile rikicin da ya ɓarke a Sokoto, Kwamishinan yan sanda na jihar Zamfara, Ayubah Elkanah, ya jagoranci taron gina zaman lafiya tare da Malamai da duk masu ruwa da tsaki a Hedkwata da ke Gusau.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa rikici ya ɓarke a Sokoto ne bayan wata dalibar kwalejin Shehu Shagari, ta yi ɓatanci ga Annabi SAW, hakan ya fusata mutane suka kasheta kuma suka ƙonata.

Kara karanta wannan

Batanci: Ku girmama addinin mutane da abinda suka yi imani da shi sai a zauna lafiya, El-Rufa'i

Taswirar jahar Zamfara.
Kashe Deborah a Sokoto: Yan sanda sun gana da Malaman Musulunci da masu ruwa da tsaki Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kwamishinan yan sandan Zamfara ya nuna jin daɗinsa bisa namijin kokarin da shugabannin addinai da masu ruwa da tsaki suka yi wajen tabbatar da abun bai shafi jihar ba.

Ya roke su baki ɗaya su ɗora daga inda suka tsaya ta hanyar wa'azin biyayya ga dokokin Addini da kuma girmama sauran mutane da ake rayuwa wuri ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Elkana ya yi kira ga iyaye da masu rikon yara su tabbata sun sa ido kan abinda ƴaƴan su ke aikata wa musamman abin da ya shafi kafafem sada zumunta.

Haka nan ya tabbatar musu da cewa hukumar yan sanda ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen samar da ingantaccen tsaro don kare rayuka da dukiyoyin mutane.

Daga ƙarshe kwamishinan ya yi kira ga al'umma su guji ɗaukar doka a hannun su, maimakon haka su kai rahoton duk wani abu da ya faru ga hukumomin tsaro.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun sake kai kazamin hari kan matafiya a hanyar Abuja-Kaduna

Abinda Mahalarta taron suka faɗa

A nasu jawabin, Malaman addini da sauran masu ruwa da tsaki sun yaba wa rundunar yan sanda bisa kiran taro da kuma kokarinsu a yanayin tsaron Zamfara.

Sun sha alwashin yin duk abinda ya dace don tabbatar da zaman lafiya ya samu gindin zama a tsakanin magoya bayansu a jihar.

A wani labarin kuma Ana zargin yan leƙen Asiri da taimaka wa yan bindiga a sabon harin hanyar Kaduna-Abuja

Jami'an tsaro sun dora alhakin kai sabon hari hanyar Kaduna-Abuja kan masu kwarmata wa yan bindiga bayanan sirri.

A cewar wani babban jami'i Imfomomi da ke zaune a kauyukan yankin ne suka jawo harin ta hanyar taimaka wa yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262