Ana zargin yan leƙen Asiri da taimaka wa yan bindiga a sabon harin hanyar Kaduna-Abuja

Ana zargin yan leƙen Asiri da taimaka wa yan bindiga a sabon harin hanyar Kaduna-Abuja

  • Jami'an tsaro sun dora alhakin kai sabon hari hanyar Kaduna-Abuja kan masu kwarmata wa yan bindiga bayanan sirri
  • A cewar wani babban jami'i Imfomomi da ke zaune a kauyukan yankin ne suka jawo harin ta hanyar taimaka wa yan bindiga
  • Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Kaduna da kwamishinan yan sanda sun ziyarci wurin da safiyar Laraba

Kaduna - Jami'an tsaro suna zargin yan leken asirin yan bindiga da taka muhimmiyar rawa wajen karyewar tsaro da sace dandazon matafiya a babbar hanyar Abuja-Kaduna da yammacin Talata.

Daily Trust ta tattaro cewa maharan da suka farmaki matafiya a hanyar da karfe 4:30 na da masaniyar lokutan da motocin Sintiri ke zagaraftu a hanyar mai tsayin kilo mita 155.

Haka nan kuma an gano cewa maharan sun samu bayanai kan lokacin zuwa da lokacin dawowar motocin jami'an tsaro da ke aikin Sintiri.

Kara karanta wannan

Gwamnan 2023: Yadda masoya APC a Sokoto ke neman ayi zaben fidda gwani na kato bayan kato

Kan hanyar Kaduna-Abuja.
Ana zargin yan leƙen Asiri da taimaka wa yan bindiga a sabon harin hanyar Kaduna-Abuja Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Wani babba daga cikin jami'an tsaro ya shaida wa wakilin jaridar cewa haɗin guiwa tsakanin Imfomomi da ke zuane a ƙuyukan yankin da yan bindiga shi ya haddasa matsalar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ƙara da cewa yan bindigan sun kaddamar da mummunan nufin su ne ƙasa da mintuna w0 bayan motocin sintirin jami'an tsaro sun wuce ta wurin.

Kwamishina ya kai ziyara wurin

Kwamishinan yan sanda na Kaduna tare da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, sun kai ziyara wurin don gane wa idonsu da safiyar Laraba.

CP ya bukaci jami'an tsaron su tashi tsaye su kara zafafa sintiri kana su bi bayan yan ta'addan domin ceto waɗan da suka sace.

Mutum nawa maharan suka sace?

Aruwan ya gaya wa jaridar cewa gwamnatin Kaduna ba zata iya tabbatar da adadin matafiyan da maharan suka sace ba amma ya ce an ɗauke motocin matafiyar zuwa ofishin yan sanda.

Kara karanta wannan

Abuja: Rayuka 5 sun salwanta a arangamar 'yan kasuwa da 'yan achaba

Bayanai sun nuna cewa wurin da yan ta'addan suka kai hari tsakanin Katari da Kurmin Kare, nan ne jami'an tsaro daga kowace hukumar tsaro ke zaune.

A wani labarin kuma Yan bindiga sun sake kai mummunan hari kan matafiya a hanyar Abuja-Kaduna

Miyagun yan bindiga sun sake kai hari kan babbar hanyar Abuja-Kaduna da yammacin nan, sun sace matafiya da dama.

Wani shaida yace yanzu haka akwai motoci da yawa waɗan da maharan suka sace mutanen da ke ciki a gefen titin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel