A Ƙyalle Nnamdi Kanu Ya RiƘa Kallon Wassanin Liverpool, Kotu Ta Faɗa Wa DSS
- Alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja, Binta Nyako, ta ce ya kamata a bai wa shugaban IPOB damar kallon wasannin kungiyar kwallon kafa ta Liverpool (FC) yayin da ya ke a tsare
- Tun ranar 25 ga watan Yunin 2021 Kanu ya ke hannun Rundunar Tsaro ta Fararen kaya (DSS) bayan an kama shi a Kenya inda aka dawo da shi kasar nan
- Yayin alkalancin, Nyako ta bukaci DSS ta bai wa Kanu damar kallon wasannin kungiyar kwallon kafa ta Liverpool musamman ganin cewa masoyin kungiyar ne tun yana da shekaru 7
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Binta Nyako, alkalin babban kotun Abuja ta ce a dinga bai wa shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu damar kallon wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool (FC) yayin da ya ke a tsare, The Cable ta ruwaito.
A ranar 25 ga watan Yunin 2021 aka kama Kanu daga kasar Kenya zuwa Najeriya inda tun bayan nan ya ke hannun Rundunar Tsaro ta Fararen Kaya (DSS).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gurfanar da Kalu gaban kotu ana zarginsa da aikata laifuka 15.
Ba a bayar da belin Kanu ba
Sai dai a ranar 8 ga watan Afirilu, Binta Nyako, Alkalin, ta zaftare laifuka 8 cikin jerin laifuka 15 da ake zarginsa da aikatawa.
A ranar Laraba, Nyako ta ki bayar da belin shugaban IPOB din.
Bayan kammala shari’ar, lauyan Kanu, Mike Ozekhome, ya yi korafi akan yadda DSS ba ta bai wa Kalu damar ganawa da lauyoyinsa tare da hana sauran lauyoyi isasshen lokacin tattaunawa da wadanda su ke karewa.
Nyako ta tunatar da Ozekhome cewa a baya ya jinjina wa DSS akan samar da katifar marasa lafiya, matashi da sauran abubuwa ga wanda ya ke karewa kuma ta bayar da umarnin samar da kula, abinci, suttura da kuma magunguna ga Kanu.
Hanyar Abuja-Kaduna: A jiya Talata kadai, mutum 20 sun kone kurmus a hadarin mota, yan bindiga sun sace 30
Yayin da ta koma kan Kanu, ta ce duk da ba shi damar sauya suttura da aka yi, shugaban IPOB din ya ci gaba da sanya kayansa samfurin Fendi.
A cewarta, shi ne ya ke son bayyana gaban kotu da kaya daya duk da kafafen sada zumunta sun sha ganinsa da wasu kayan na daban.
Alkali ta bayar da umarnin a bai wa Kanu damar kallon duk wani wasan kwallon da za a yi da Liverpool
Alkalin ta ci gaba da jan sa da raha inda ta ce tana goyon bayan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, daga nan ta tambayi Ozekhome wanda shi ma ya ce yana goyon bayan Liverpool.
Daga nan Nyako ta tambayi Kanu ko ya na mara wa kungiyar Chelsea baya, inda ta ce:
“Kai dan wanne kungiya ne?”
Sai Kanu ya amsa ta inda ya ce:
“Ni dan kungiyar Liverpool ne tun ina da shekaru 7 da haihuwa.”
Ta bukaci lauyan DSS da su dinga ba Kanu damar kallon wasan fidda gwanin da za a yi tsakinin kungiyar Real Madrid da Liverpool ko kuma duk wani wasa da za a yi da kungiyar.
A cewarta:
“Wajibi ne ku ba shi damar kallon wasannin kwallon kafar da su ke yi.”
Daga nan jami’in DSS ya ce dama ana ba Kanu damar kallon talabijin a ofishinsa.
Asali: Legit.ng