Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari zai yanke hukunci kan Ministocin da suka janye takara
- Babu tabbaci game da komawar Ministocin da suka janye burinsu na takara bakin aiki yayin da Lai Muhammed ya ce bai san halin da ake ciki ba
- Ministan labarai da Al'adu ya ce shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ne kaɗai ke da ikon yanke hukunci kan makomar su
- Ya nemi manema labari su bashi isasshen lokaci domin ya nemi bayani daga bakin shugaban kasa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Har yanzun tana ƙasa tana dabo kan matsayin wasu mambobin majalisar zartarwa na gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, waɗan da suka janye burinsu na takara a 2023.
Punch ta rahoto cewa Ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ya ce shugaba Buhari ne kaɗai zai yanke hukunci kan makomar su.
Zuwa yau Laraba, Ministar harkokin mata, Pauline Tallen, Antoni Janar na ƙasa kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, ƙaramin Ministan albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva da Ministan kwadugo, Chris Ngige, sun janye daga takara.
Da yake amsa tambayoyin manema labaran gidan gwamnati jim kaɗan bayan taron FEC na Laraba, Muhammed, ya ce akwai bukatar ya ji daga Buhari kan ko ya amince ministocin su koma bakin aiki ko akasin haka.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar ministan:
"Komawar Ministocin bakin aiki ko akasin haka, ina bukatar ku bani lokaci isasshe saboda na zo muku da ainihin bayanin halin da ake ciki. A halin yanzu ina bukatar na bincika."
"Ina da bukatar na sami tabbaci daga shugaban ƙasa kan halin da ake ciki, domin hukunci na ƙarshen kan wanda zai tafi da kuma wanda zai koma bakin aiki yana hannun Buhari."
Sun halarci taron FEC
Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa an hangi Malami a wurin taron FEC na yau Laraba yayin da Sylva da Tallen suka shiga taron ta fasahar zamani daga Ofisoshinsu da ke Abuja.
Ministan Kwadugo da rage zaman kashe wando, Chris Ngige, ba ya ƙasa ya je Durban, kasar Afirka ta kudu, inda ya halarci taron duniya na kungiyar kwadugo ta ƙasa da ƙasa, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
A wani labarin kuma Gwamnan Arewa ya rantsar da sabbin Kwamishinoni 7 a jiharsa, ya nemi su tashi tsaye
Gwamna Bello na jihar Neja ya rantsar da sabbin kwamishinoni Bakwai biyo bayan aje aikin masu neman takara.
Bello ya roke su da su tashi tsaye wajen kokarin sauke nauyin da aka ɗora musu musamman a irin wannan lokacin me kalubale.
Asali: Legit.ng