Abuja: Rayuka 5 sun salwanta a arangamar 'yan kasuwa da 'yan achaba
- Mummunan rikici ya barke a tsakanin 'yan kasuwa da 'yan achaba a yankin AMAC a Abuja inda aka rasa wasu rayuka da gidaje
- Ganau ya sanar da yadda 'yan kasuwa suka far wa dan achaba sakamakon tukin ganganci da yayi har ya halaka fasinja daya
- Tarzomar ta yi sanadin rasa rayuka biyar tare da kone wasu gidaje masu yawa a yankin wanda yanzu lamarin ke komawaa rikicin kabilanci
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
AMAC, Abuja - A kalla rayukan wasu mutum biyar ne suka salwanta yayin da gidaje masu yawa suka kone sakamakon arangama tsakanin 'yan kasuwa da 'yan acaba a kwaryar birnin Abuja.
Wani mazaunin yankin ya sanar da Daily Trust cewa, hatsari ne ya ritsa da dan achaba wanda hakan ya janyo tarzoma a yankin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Mutane biyar da na sani suka rasu a mummunan al'amarin. Muna ta kiran jami'an tsaro domin su kawo dauki amma a banza," a cewar mazaunin yankin wanda ya bukaci a boye sunansa.
"Muna cikin tsananin tashin hankali ganin yadda rikicin ke rikidewa yana komawa na kabilanci."
An gaza tantance yawan gidajen da suka kone
Har a yayin rubuta wannan rahoton, ba a tantance yawan mutanen da lamarin ya shafa ba.
'Yan kasuwan sun kai wa dan achaban hari bayan sun zarge shi da tukin ganganci wanda ya yi sanadin rasa rayuwar wani fasinja.
Abokan aikin dan achaban sun hanzarta zuwa domin kai masa dauki daga maharansa wanda hakan yasa rikicin ya rincabe.
Wata majiya ta ce direban tirelan da ya mitsike wasu fasinjoji har suka mutu ne aka kai wa hari yayin da wasu suka hanzarta kai masa dauki.
Daily Trust ta ruwaito cewa, jami'an tsaro sun hanzarta zuwa wurin domin dakile cigaban tarzomar.
Wannan rikicin na Abuja na aukuwa ne a ranar da Gwamna Sanwo-Olu na jihar Legas ya haramta achaba a wasu kananan hukumomin jihar sakamakon kashe wani injiniya da aka yi.
An halaka Injiniyan ne tare da kona shi a yankin Lekki a ranakun karshen mako da suka gabata.
Gwamnati Ta Haramta Yin Acaba a Ƙananan Hukumomi 6 a Legas
A wani labari na daban, gwamnatin Jihar Legas ta haramta yin haya da babur wato acaba a kananan hukumomi shida na jihar, rahoton Channels Television.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas ne ya sanar da hakan yayin da ya ke yi wa hukumomin tsaro a jihar jawabi a ranar Laraba, rahoton The Cable.
Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Ikeja, Surulere, Eti Osa, Lagos Mainland, Lagos Island da Apapa.
Asali: Legit.ng