Tashin Hankali a Kano: Iyaye sun fara tururuwar kwashe 'ya'yan su bayan abu ya Fashe a Kano

Tashin Hankali a Kano: Iyaye sun fara tururuwar kwashe 'ya'yan su bayan abu ya Fashe a Kano

  • Fashewar tulun Gas kamar yadda kwamishinan yan sanda ya ce ya tada hankulan iyayen kananan yara da ke zuwa makaranta
  • Bayan faruwar lamarin a Sabon Garin jihar Kano, wasu iyayen yara suka riƙa zuwa suna kwashe ƴaƴan su daga makarantun yankin
  • Yayin haka ne kuma wasu yan iskan garu suka yi amfani da damar wajen shiga gidaje da shagunan mutane

Kano - Yanayi ya canza zuwa tashin hankali a yankin Sabon Gari da ke jihar Kano bayan wani abu da ake zaton Bam ne ya tashi da safiyar nan ta ranar Talata.

Daily Trust ta ruwaito yadda fashewar abun wanda ya a faru a bayan wata makarantar Firamare ya jefa mutane cikin tsoro da tashin hankali a Anguwar.

Kara karanta wannan

Da zafi-zafi: Hotunan Osinbajo yayin da ya ziyarci wajen da tukunyar gas ta fashe a Kano

Fashewa a Kano.
Tashin Hankali a Kano: Iyaye sun fara tururuwar kwashe 'ya'yan su bayan abu ya Fashe a Kano Hoto: tvcnewsng
Asali: Twitter

Bayan rahoton da ya yaɗu a kafafen sada zumunta wanda ya yi ikirarin hari ne aka kai makaranta, iyaye sun fara garzayawa makarantun da ke yankin suna ɗauke ƴaƴan su.

Mutane sun rufe shaguna, yayin da wasu rahotanni suka nuna cewa yan daba sun soma amfani da yanayin da mutane ke ciki suna shiga gidaje da shaguna.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Akwai wasu bidiyoyi da suka nuna ɗalibai na gudu kayan makarantar da ke jikinsu da alamun jini a jiki sun watsu a kafafen sada zumunta.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa jami'an ba da agaji sun tabbatar da gano gawarwakin mutum 9, waɗan da lamarin ya yi ajalin su.

Rundunar yan sanda a jihar Kano ta ce tukunyar iskar Gas ce ta fashe ba harin Bam bane kamar yadda mutane ke yaɗa jita-jita.

Yan bindiga za su farmaki kananan hukumomi 9

Kara karanta wannan

Fashewar tulun iskar gas: Hukuma ta bayyana adadin mutanen da suka mutu a iftila'in Kano

A wani labarin kuma Yan bindiga sun aike da sakon sunayen kananan hukumomi 9 da zasu kai hari

Miyagun yan bindiga sun aike da wasika ɗauke da jerin sunayen wasu kananan hukumomi 9 da zasu kai hari nan ba da jimawa ba.

Hakan ya zo ne awanni bayan wasu mahara sun farmaki karamar hukuma da Kotu, inda suka aikata ɓarna mai yawa duk a Anambra.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262