Sokoto: Wani Malami ya yi alkawarin daukar nauyin iyayen ɗalibar da ta zagi Annabi
- Wani babban Malamin Coci, Fasto Chibuzor Chinyere, ya yi alƙawarin share wa iyayen Deborah hawayensu bayan rasa ɗiyarsu
- Faston ya ce a sanar musu zai ɗauki nauyin karatun ragowar ƴaƴan su, zai ba Mahaifin aiki kuma zai bude wa mahaifiyar shago
- Deborah da ke karatu a kwalejin Shehu Shagari ta rasa rayuwarta ne bayan ta yi kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW)
Babban mai kula da Cocin Omega Power Ministries, Fasto Chibuzor Chinyere, ya yi tayin ɗaukar nauyin karatun ragowar yan uwan Deborah Samuel, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto
Deborah, wacce ke karatu a makarantar horad da malamai ta tunawa da Shehu Shagari a Sokoto, ɗalibai sun jefe ta kuma suka ƙona ta bayan ta yi munanan kalamai ga Annabi Muhammad (SAW).
Mahaifiyar Deborah, Alheri Emmanuel, a ranar Lahadi ta ce ba zata sake tura ragowar 'ya'yanta makaranta ba saboda kisan gillan da aka yi wa ɗiyarta.
Ta ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ba abun da nake bukata, banson komai abu ɗaya da na sani shi ne ba zan sake tura ƴaƴana makaraanta ba."
Haka nan, Mahaifin dalibar, Garbaanuel, wanda ke aikin gadi a ma'aikatar ruwa da tsafta ta jihar Neja, ya koka kan cewa ya yi amfani da dukkan tanadin shi wajen tura ɗiyarsa ta farko makaranta.
Alƙawurran da Faston ya ɗauka
Da yake martani kan maganganun su, Malamin Cocin ya yi alkawarin samarwa iyayen Deborah aiki kuma zai inganta rayuwarsu ta yadda ba zasu sake wahala ba.
Babban Faston ya ce:
"Yanzu na gama kallon Bidiyon kalaman iyayen Deborah inda naji suna cewa ba zasu sake tura yaran su makaranta ba, Allah ya kiyaye. Duk me lambar su ya faɗa musu cewa Ni, babban mai kula da Cocin OPM zan dawo da su Patakwal."`
"Zasu zauna a ɗaya daga cikin gidajen OPM kyauta, ba zasu biya ko sisi ba kuma dukkan 'ya'yan da suka haifa za su yi karatu kyauta a makarantun OPM."
"Zan samar wa Mahaifin aiki sannan kuma zan buɗe wa matarsa shagon da zata cigaba da sana'a, Dan Allah ku tuntuɓe su nan take."
Tun a farko Malamin Cocin ya yi tayin ɗaukar nauyin karatu ga wasu jami'an tsaro biyu a Najeriya waɗan da aka sallama daga aiki bayan ganin bidiyo suna rawa lokacin aiki.
A wani labarin kuma Bayan Debora a Sokoto, wata Naomi Goni ta sake kalaman batanci ga Annabi SAW a Borno
Yayin da aka fara jitar-jitar wata kirista ta sake kalaman batanci ga Annabi, Jami'an tsaro sun shirya ba da tsaro a birnin Maiduguri.
Rahoto ya nuna cewa wacce ake zargi da yin ɓatancin ta taɓa zama a jihar Borno, amma ta jima da barin jihar.
Asali: Legit.ng