Rikici: 'Yan sanda sun kwamushe mutum 4 bisa laifin kisa da kone wani mutum a kan N100

Rikici: 'Yan sanda sun kwamushe mutum 4 bisa laifin kisa da kone wani mutum a kan N100

  • Rundunar 'yan sanda ta kame wasu mutum hudu da ake zargi da kashe wani mawaki a jihar Legas tare da kone shi
  • Wannan lamari ya faru ne yayin da rikici ya barke tsakanin abokan wanda aka kashen da wasu 'yan acaba
  • Wannan lamari ya haifar da tada kura a kafafen sada zumunta, inda wasu suke nemawa mawakin adalci

jihar Legas - ‘Yan sanda a jihar Legas sun kama wasu mutane hudu da ake zargin sun yi wa wani David Imoh mai shekaru 38 kisan gilla ta hanyar kone shi a yankin Lekki Phase One na jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, kama mutunen a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai wasika Zamfara bayan kashe manoma 7 da Limamin masallacin Juma'a

Yadda aka kame wadanda suka kashe mawaki a Legas
Rikici: 'Yan sanda sun kwamushe mutum 4 bisa laifin kisa da kone wani mutum a kan N100 | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A cewarsa:

“Al’amarin ya faru ne a ranar 12 ga watan Mayu, 2022. An kama mutane hudu a ranar game da wannan aika aika. Muna kan hanyar kama mutum na biyar, yanzu muna nemansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Wanda aka kashe shine David Imoh, mai shekara 38. Za a gurfanar da wadanda ake zargin idan an kama su. Za mu tabbatar an gurfanar da su gaba daya domin su zama darasi ga wasu.”

A cewar Mista Hundeyin, wanda Sufeto na ‘yan sanda ne, ba a yarda da daukar doka a hannu a jihar Legas ba, ya kuma gargadi jama’a da su guji irin haka.

Ya kara da cewa:

"Kada ku dauki doka a hannunku."

A baya NAN ta tattaro cewa wasu da ake zargin 'yan acaba ne da ke aiki a yankin Lekki Phase One sun lakada wa David dukan tsiya a kan rikicin da ya barke kan N100.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun yi garkuwa da wasu 20 a Kaduna

An ce, duk da bayanin da Philip ya yiwa 'yan acaban, sun dage cewa dan Yahoo ne wanda har ta kai suka cinna ma David wuta, inji rahoton This Day.

An samu cewa rashin jituwar ta haifar da hargitsi tsakanin David da daya daga cikin 'yan acaban.

Tashin hankali yayin da 'yan acaba suka kashe tare da kone wani akan N100

A wani labarin, 'yan Najeriya sun bukaci a nemawa wani injiniyan sauti mai suna David adalci, wanda wasu da ake zargin 'yan acaba ne suka yi masa duka tare da kona shi a unguwar Admiralty da ke Lekki a jihar Legas.

Punch Metro ta tattaro cewa abokan aikin injiniyan, Frank da Philip sun hau acaba zuwa wani wurin da ke Admiralty Way, Lekki, inda David ke shirya wasan kwaikwayo.

An ce dan acaban ya kai mutanen biyu ne zuwa inda aka nufa sai kawai wata takaddama ta kaure kan N100 tsakanin dan acaban da abokan David.

Kara karanta wannan

Batanci Ga Annabin Rahma (SAW), Dr Sani Umar Rijiyar Lemo

Asali: Legit.ng

Online view pixel