2023: Kotu ta aika dan takarar gwamna na PDP gidan gyara hali

2023: Kotu ta aika dan takarar gwamna na PDP gidan gyara hali

Rivers - Babbar kotun jihar Ribas, a ranar Litinin, 16 ga watan Mayu, ta saka ranar sauraron bukatar bayar da belin dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Ribas, Hon. Farah Dagogo, wanda ke tsare.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa alkalin kotun, Mai shari’a Chinwendu Nworgu, ya tsayar da ranar Juma’a, 20 ga watan Mayu domin zama kan lamarin.

Don haka, Nworgu, ya yi umurnin mayar da Dagogo wanda ya kuma kasance dan majalisar wakilai gidan gyara hali da ke Port Harcourt.

Asali: Legit.ng

Online view pixel