Ganduje ya ɗauki mataki bayan shugaban ma'aikatan fadar gwamnati ya koma NNPP
- Bayan sauya shekar shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Kano zuwa NNPP, Ganduje ya ba da umarnin a kula harkokin ofishin
- Gwamnan ya ba shugaban ma'aikatan Kano, Usman Bala, ya kula da ofishin kafin ya maye gurbinsa saboda ya na da kwarewa a fannin
- Tsohon shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin, Makoda, ya aje aikinsa tare da sauya sheka daga APC zuwa NNPP da ake ya yi
Kano - Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya umarci shugaban ma'aikata, Usman Bala, ya rike ofishin tsohon shugaban ma'aikatan fadar gwamnati, Ali Haruna Makoda.
Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne biyo bayan sauya shekar Makoda daga APC zuwa jam'iyyar NNPP mai kayan marmari.
Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton yadda shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin ya aje aikinsa, kana ya fice daga APC ya koma jam'iyyar da ake ya yi wato NNPP.
Mista Makoda, wanda tun farko gwamna Ganduje ya ki amincewa da murabus dinsa, ya na da burin neman kujerar ɗan majalisar wakilai a 2023, inji wata majiya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A wata sanarwa, kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Muhammad Garba, ya ce Gwamna Ganduje ya umarci Usman ya kula da harkokin ofishin shugaban ma'aikatan gidan gwamnati.
Kwamishinan ya ce gwamna Ganduje ya ɗauki wannan matakin ne kafin zaƙulo wanda zai maye gurbin Makoda, wanda ya fice daga APC.
A wani sashin sanarwan, Muhammad Garba ya ce:
"Gwamna Ganduje ya nuna kwarin guiwarsa da fatan cewa za'a samu kyakkyawar kula da tafiyar da harkokin ofishin daga hannun Usman, kasancewar ya taɓa rike muƙamin."
Makoda ya yi aiki a matsayin kwamishinan Muhalli a zangon mulkin Ganduje na farko, daga bsani ya koma ofishin shugaban ma'aikatan gwamnan jihar Kano.
Batun sauya shekara Shekarau ya yi zafi a Kano
A wani labarin kuma Dirama a Kano yayin da tawagar Kwankwaso ta dira gidan Shekarau awanni bayan tafiyar Ganduje
Siyasar Kano ta ƙara rikicewa musamman tsakanin gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau.
Bayan ziyarar Ganduje gidan Shekarau don hana shi komawa NNPP, Kwankwaso ya tura tawaga kafin zuwansa gidan Shekarau.
Asali: Legit.ng