Dokar kulle: Bishop Kukah ya yabawa matakin Tambuwal, ya karyata batun kai hari gidansa
- Limamin addinin kirista na jihar Sokoto, Bishop Mathew Kukah, ya yi martani a kan saka dokar kulle da gwamnatin jihar ta yi
- Bishop Kukah ya yabawa Gwamna Aminu Tambuwal a kan wannan mataki na gaggawa da ya dauka domin kwantar da tarzoman da ya taso, ya kuma karyata batun kai hari gidansa
- Matasa dai sun gudanar da zanga-zanga a birnin jihar sakamakon kama wasu da aka yi kan kisan wata daliba mai suna Deborah Samuel bayan ta yi batanci ga Annabi
Sokoto - Babban Limamin Cocin Katolika na Diocese na Sokoto, Mathew Kukah, ya yabawa gwamnan jihar, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal kan ayyana dokar kulle na awa 24 da ya gaggauta yi domin kwantar da zanga-zangar da ke gudana a jihar, rahoton Vanguard.
Da farko masu zanga-zangar sun farmaki cocin Holy Family Catholic Cathedral a hanyar Bello Road da St. Kevin’s Catholic Church, Gidan Dere, inda suka faffasa wunduna da wata tashar mota a harabar.
Idan za ku tuna gwamnan ya shirya zuwa jihohi shida don tuntubar da ke gudana kan kudirinsa na son takarar shugaban kasa. Sai dai kuma, ya soke tafiyar don tabbatar da dawo da zaman lafiya a jihar.
Ya bayyana cewa:
“Zaman lafiyar jihar ya fi muhimmanci bisa ga kudirin takararsa."
Da yake martani, Kukah, a cikin wani jawabi dauke da sa hannun daraktan hulda da jama’a na cocin Kotolika da ke Sokoto, Reverend Father Christopher A. Omotosho, ya yabawa Gwamna Tambuwal kan matakan gaggawa da ya dauka.
“A wani martani, babban limamin Katolika na Sokoto, Reverend Mathew Kukah, ya yabawa gwamnan na jihar Sokoto, Aminu Tambuwal kan daukar matakin gaggawa ta hanyar sanya dokar kulle na awa 24 don tsayar da zanga-zangar."
Ya kuma yabawa hukumomin tsaro kan gaggauta shiga lamarin da suka yi domin hana yaduwar zanga-zangar.
Bishop Kukah, a cikin sanarwar, ya kuma yi watsi da rade-radin kai ma gidansa hari, Daily Trust ta rahoto.
Ya ce:
“Sabani labarin da ke yawo, muna fatan karyata cewa an kai wani hari kan gidan Bishop Matheny Hassan Kukah.”
Malamin addinin ya kuma roki kiristoci da su ci gaba da bin doka da addu’an dawowar zaman lafiya a jihar.
Ya kara da cewa:
"An dakatar da duk wani harkoki a cikin babban birnin Sokoto har sai an dage dokar kullen."
Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi
A baya mun ji cewa Mathew Kukah, ya yi Allah-wadai da kisan wata dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto a yau Alhamis.
Ya kuma yi kira da a kwantar da hankali kan lamarin, yana mai cewa lamarin ba na addini bane, inji rahoton Channels Tv.
A cewar rundunar ‘yan sanda, an zargi Deborah Samuel, ‘yar matakin karatu na biyu, da yin wani rubutu a dandalin sada zumunta na yanar gizo wanda ya nuna alamun batanci ga manzon Allah (SAW).
Asali: Legit.ng