An birne Deborah, dalibar da aka kashe kan batanci ga Manzon Allah (SAW)
- Iyayen Deborah Samuel sun birneta ranar Asabar a jihar Neja bayan kisan da aka yi mata a Sokoto
- Deborah Samuel ce dalibar kwaljin ilimi a Sokoto da tayi kalaman batanci kan Manzon Allah (SAW)
- Mutane sun tofa albarkatun bakinsu kan labarin da yayi sanadin mutuwar Debora a Sokoto
Neja - An birne Deborah Samuel, dalibar kwalejin ilmin Shehu Shagari da aka kashe a jihar Sokoto kan laifin kalaman batancin ga Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata gareshi).
TheNation ta ruwaito cewa an birne Deborah ne a mahaifarta, Tunga Magajiya, dake karamar hukumar Rijau a jihar Neja.
An birneta misalin karfe 6:30 na yamma a makabartar Kirista dake Tunga Magajiya.
Da farko matasan garin Tunga Magajiya sun ki amincewa a birneta inda suka ce gwamnatin jihar Sokoto ya kamata su dau nauyin jana'izar.
Amma babba yayanta wanda Fasto na a cocin ECWA, Emmanuel Maaji, ya jagoranci bizneta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
'Mun bar wa Allah' Iyayen ɗalibar da ta zagi Annabi a Sokoto sun yi magana bayan binneta
Mahaifin Debora Samuel, wacce aka kashe kan zargin ɓatanci a Sakkwato, Emmanuel Garba, ya bayyana cewa iyalansa sun ɗauki abun da da ya faru a matsayin kaddara daga Allah.
A ranar Asabar aka birne gawar Debora a mahaifarta da ke Tungan Magajiya. ƙaramar hukumar Rijau a jihar Neja, kamar yadda The Cable ta rahoto.
A wata zantawa da Dailypost, Garba, ya ce iyalansa sun shiga ƙunci bisa kisan Debora, amma ya ce ba abin da zasu iya yi game da lamarin.
Garba ya kuma bayyana yadda ya biya N120,000 na ɗakko gawarta daga Sakkwato zuwa Neja bayan ya fahimtar da gwamnati ta barshi ya birne gawar ɗiyarsa.
Asali: Legit.ng